Da Ɗumi-Ɗumi: Sojoji sun hallaka sabon shugaban mayaƙan ISWAP, Malam Baƙo

Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Manjo Janar Babagana Mongonu (mai ritaya) ya sanar da mutuwar Malam Bako, wanda ya maye gurbin Abu Musab Al-Barnawi, shugaban ƙungiyar mayaƙan ISWAP.

Mongonu ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai na fadar shugaban ƙasa kan sakamakon ganawar shugabannin hafsoshin tsaro, wanda shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya jagoranta, a fadar gwamnati da ke Abuja, ranar Alhamis.

  • Da Ɗumi-Ɗumi: Sojoji sun hallaka sabon shugaban mayaƙan ISWAP, Malam Baƙo
  • Ƴan bindiga sun dasa bama-bamai a hanyar jirgin ƙasa Abuja-Kaduna

Ya kuma bayyana cewa wanda ya gaji Abu Musab, Malam Bako an kashe shi tare da wani fitaccen ɗan ƙungiyar ISWAP.

“Sojoji sun yi kyakkyawan aiki saboda a cikin wata ɗaya sun hallaka jagoran ISWAP, wato Abu Musab Al-barnawi .

“Kwanaki biyu da suka gabata, an kuma kashe wanda ya gaje shi, Malam Bako, ɗaya daga cikin fitattun shugabannin ISWAP.

“Don haka, ayyukan da sojojin ke gudanarwa a yankunan Arewacin ƙasar nan ya zama matsin lamba ga ISWAP, Boko Haram da kuma kungiyar ISGS.”

Idan ba a manta ba a makon jiya babban hafsan tsaro, Laftanar Janar Lucky Irabor ya faɗawa manema labarai na fadar gwamnati cewa sojoji sun kashe shugaban ISWAP, Abu Musab Al-barnawi.

Irabor ya ce, “Zan iya tabbatar muku da cewa Abu Musab ya mutu. Ya kuma tabbata matacce. ”