DA ƊUMI-ƊUMai: Sojoji da Ƴan Sa Kai sun kuɓutar da ɗaliban FGC Birnin Yawuri

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Sojoji tare da gudunmawar ƴan sa kai sun kuɓutar da wasu daga cikin ƴan makarantar Gwamnatin Tarayya ta garin Birnin Yawuri da aka sace a jiya Alhamis.

Rahotanni dake fitowa daga yankin Yauri da Zuru sun ce sojojin sun yi wa ɓarayin ƙofar rago ne a ranar Alhamis da daddare a tsakanin dajin Rijau da Dirin Daji.

Wasu majiyoyi sun shaidawa Hausa Daily Times cewa an kashe a ƙalla ƴan ta’adda 100 a yayin gumurzun.

Majiyoyin sun ce an yi bata kashi sosai tsakanin dakarun haɗin gwiwa na sojoji da ƴan sa kai da kuma ɓarayin dajin a ƙaramar hukumar Sakaba dake jihar Kebbi.

A halin yanzu, an bayyana cewa ɗalibai da Malaman makarantar da aka kubutar na ƙaramar hukumar Sakaba.