DA ƊUMI ƊUMIN SA: Kotu ta umarci kungiyar ASUU ta janye yajin dole, ɗalibai su koma makaranta

Kotun ‘Industrial’ a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya ta yanke hukuncin umartar kungiyar malaman jami’o’i su janye yajin aikin da suke yi su koma dalibai su koma makaranta maza-maza.
Wannan na kunshe ne a hukuncin da kotun ta yanke wanda mai shari’a Polycarp Hamman ya karanta ranar Laraba.
Lauyan da ke kare gwamnatin tarayya ya roki kotu ta tilasta wa ASUU ta janye yajin aiki sai an kammala tantance korafin gwamnati wanda ministan kwadago ya shigar.
Kungiyar ASUU ta fara yajin aiki tun watan Faburairun 2022.
Dalibai sun shafe watanni 7 cur kenan suna zaune gida.