Da Ɗumi-Ɗumi: Ƴan bindiga sun sace Sarkin Bungudu na jihar Zamfara

Rahotanni da muke samu sun tabbatar da da cewa wasu da ake zargin ƴan bindiga ne masu garkuwa sun sace Sarkin Bungudu na jihar Zamfara Alhaji Hassan Attahiru Bungudu tsakanin hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Wata majiya daga da ke da kusanci da Sarkin ta shaidawa Hausa Daily Times cewa ƴan bindigan sun tafi da Sarkin da jami’an tsaron sa da duk wanɗan da suke cikin motar sa.

Lamarin ya faru ranar Talata a yayin da Sarkin tare da jerin gwamnon motocin tawagarsa suka nufi babban birnin tarayya Abuja a tsakanin hanyar Kaduna zuwa Abuja.

  • Da Ɗumi-Ɗumi: Ƴan bindiga sun sace Sarkin Bungudu na jihar Zamfara
  • Yadda wani hamshaƙin ɗan kasuwa ya yiwa ƴar shekara 14 ciki a Kano

Sai dai izuwa lokacin haɗa wannan rahoton babu sanarwa a hukumance daga jami’an tsaro dangane da faruwar lamarin.

An wallafa wannan Labari September 14, 2021 9:33 PM