CUTAR HEPATITIS: Yadda Najeriya ke yi wa yakin dakile yaduwar cutar tafiyar hawainiya duk da kisar da ta ke yi

A shekarar 2016 ne kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta kaddamar da wasu hanyoyi da za su taimaka wajen rage yaduwar cutar hepatitis a duniya.

Bisa ga wadannan hanyoyi da aka tsara hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ita kuma ta tsara da maida hankali wajen gani an raye yaduwar cutar kwata-kwata daga shekarar 2016 zuwa 2030.

A watan Faburairun 2020 a taron dakile yaduwar cutar da aka Yi a Cairo kasar Masar gwamnatocin kasashen Afrika tattauna yadda za su kawo karshen yaduwar cutar ta kowacce hanya.

A Najeriya mutum kashi 12% daga cikin mutum miliyan 200 na dauke da cutar hepatitis B sannan kashi biyu bisa dari na dauke da hepatitis C.

Duk da haka babu wani rawar da gwamnatin Najeriya ta taka ko za ta taka wajen dakile yaduwar cutar daga yanzu zuwa shekarar 2030 da ake sa ran an gama da cutar.

Cutar Hepatitis

Wata malama dake koyarwa a jami’ar Legas Kuma likitar da ta kware wajen sanin cutar hepatitis a asibitin Emuobor Odeghe ta bayyana cewa hepatitis cuta ce dake yin illa ga huhun mutum.

Emuobor ta ce akwai nau’ukan cutar da dama amma an fi kamuwa da nau’in hepatitis A da B a ne.

Ta ce nau’in hepatitis B ana iya kamuwa da ita idan mai dauke da cutar ya yi tari a cikin mutane ba tare da ya rufe bakinsa ba ko idan zufa ko yawun Mai dauke da cutar ya shiga Baki ko wani sashen jikin mutum.

Hepatitis A ya fi nau’in hepatitis C da kanjamau yin lahani ga mutum.

Emuobor ta ce mace mai cikin dake fama da cutar na iya harba wa dan dake cikin ta cutar.

Abin da sakamakon bincike ya nuna game da yaduwar cutar

Sakamakon binciken WHO ya nuna cewa a cikin sakan 30 hepatitis na yin ajalin mutum daya a duniya kenan a rana cutar na yin ajalin mutum 3,600 a duniya.

Binciken ya nuna cewa hepatitis B da C nau’ukan cutar da aka fi kamuwa da na yin ajalin mutum miliyan 1.1 sannan wasu mutum miliyan 3 na kamuwa da cutar a duniya duk shekara.

A yanzu mutum miliyan 325 ne ke kamuwa da cutar a duniya.

Daga cikin wannan yawa kashi 26% ko Kuma mutum miliyan 90 na dauke da cutar a Afrika.

Matakan dakile yaduwar cutar da Najeriya ta dauka

Ministan lafiya Osagie Ehanire ya bayyana cewa mutum miliyan 20 ne ke dauke da hepatitis B da C a kasar nan.

Ehanire ya ce gwamnati na kokarin ganin ta Samar da maganin rigakafin cutar domin dakile yaduwar cutar kafin nan da shekarar 2030.

Sai dai wani likitan cutar hepatitis Kuma farfesa dake aiki da asibitin Babcock dake Ilishan Remo jihar Ogun Abiodun Jemilohun ya ce sakamakon bincike da ya fito a kwanaki nan ya nuna cewa mutum miliyan 12 na fama da hepatitis B, Kashi 2% na fama da hepatitis C sannan idan haka hada za a samu jimlar mutum miliyan 24 zuwa 25 dake dauke da cutar a Najeriya.

Matakan dakile yaduwar cutar da duniya ta dauka

Shugaban WHO Tedros Ghebreyesus yayi kira ga kasashen duniya da su mike tsaye wajen ganin sun cimma burin rage yaduwar cutar nan da 2030.

Ghebreyesus ya ce burin WHO shine rage yaduwar Hepatitis B da C zuwa kashi 90% da yawan mutanen da cutar ke kashewa zuwa kashi 65% daga 2016 zuwa 2030.

Bincike ya nuna cewa mutum sama da miliyan 250 na dauke da cutar a duniya sannan kashi 80% daga ciki basu iya samun maganin cutar.

A shekaran 2020 a Cairo kasar Masar gwamnatocin kasashen Afrika sun tsara wasu hanyoyi da za su taimaka wajen rage yaduwar cutar.

A taron gwamnatin kasar Masar ta yi alkawarin samar da maganin Hepatitis C wa mutum miliyan 1 a Afrika.

A yanzu haka kasar Masar ta tallafawa mutum sama da 50,000 da maganin cutar a kasashen Kudancin Sudan, Eritrea da Chad.

Kasashen Rwanda, Uganda da Jamhuruyyar kasar Benin na yi wa mutane gwaji da bada maganin cutar kyauta a kasashen su sannan wasu kasashen Afrika 16 sun fara bin sawun haka a kasashen su.

Kasashe kamar su Uganda da Jamhuruyyar Benin na yi wa mutane gwajin Hepatitis kyauta a kasashen su, kasar Masar ta rage farashin maganin cutar a kasar amma Najeriya ta ƙasa rage farashin yin gwaji da samun maganin cutar.

Mafita

WHO ta yi kira ga kasashen duniya da su tilasta wa mutane yin gwajin cutar a kasashen su cewa barin cutar na ci gaba da yaduwa ka iya zama babban kalubale ga fannin kiwon lafiya a duniya.

Jemilohun da Mrs Odeghe sun yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta mai da yin gwajin cutar kyauta sannan ta rage farashin samun kula domin hakan zai taimaka wa mutanen dake fama da cutar samun kula yadda kamata.

Jemilohun ya kara da cewa gwamnati za ta iya yi wa mutane gwajin Hepatitis tare da gwajin cutar kanjamau domin yin haka zai taimaka wajen gano mutanen dake dauke da cutar a kasar nan.

“Yi wa mutane gwajin Hepatitis tare da gwajin kanjamau zai taimaka wajen dakile yaduwar cutar ganin cewa wasu magungunan kanjamau na yin maganin Hepatitis.