CUTAR DIPHTHERIA: Kano ce a gaba, mutum 123 sun rasu, 38 na kwance a asibiti

Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta bayyana cewa mutum 123 sun kamu da cutar Diphtheria sannan cutar ta yi ajalin mutum 38 a jihohi hudu a kasar nan.
NCDC ta ce bisa ga alkaluman yaduwar cutar da ta fitar na ranar 22 ga Janairu jihar Kano ce gaba da ke da mutum 100 da suka kamu sannan mutum 32 sun mutu. Na biye da ita ita ce jihar Yobe inda mutum 17 suka kamu sannan mutum 3 sun mutu.
Shugaban hukumar NCDC Ifedayo Adetifa wanda Shugaban aiyukka na musamman Priscillia Ibekwe ta wakilta a taron da ma’aikatar lafiya ta shirya ranar Litini a Abuja ya sanar da haka.
Ibekwe ta ce jihar Legas ta samu mutum biyar da suka kamu mutum uku sun mutu, jihar Osun mutum daya babu wanda ya mutu.
Hukumar NCDC ta ce ta hada hannu da jihohin da cutar ta bullo domin Samar da magungunan cutar sannan ta fara horas da jami’an lafiya domin inganta yin gwajin cutar da kula da wadanda suka kamu da cutar.
Ministan lafiya Osagie Ehanire ya ce kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ba ta yi sanarwa game da bullowar cutar ba amma NCDC na gudanar da bincike musamman kan baki da ‘yan Najeriya da suka ziyarci kasar.
Cutar Diphtheria
Cutar Diphtheria cuta ce da kwayoyin cutar bacteria mai suna ‘Corynebacterium’ ke haddasa ta.
Cutar ya fi kama yara da manya musamman wadanda ba su yi allurar rigakafin cututtuka da ake Yi wa yara ba.
Cutar kan kama makogwaro, hanci sannan wasu lokuta fatar mutum.
Cutar ya fi yaduwa idan ana yawan zama kusa da wadanda suke dauke da ita, idan mai dauke da cutar ya rika yin tari ko atishwa a tsakanin mutane.
Alamun cutar sun hada zazzabi, yoyon hanci, ciwon makogwaro, idanu su yi jajawur, tari da Kumburin wuya.
Wasu lokuta mai fama da cutar zai rika ganin wasu farin abubuwa na fitowa a kusa da makogwaro wanda ke hana mutum iya yin numfashi.
Hanyoyin gujewa kamuwa da cutar
1. Yin allurar rigakafi.
2. Saka takunkumin fuska musamman idan za a shiga cikin mutane.
3. Toshe baki da hanci idan za a yi tari ko atishwa.
4. Tsaftace muhalli, wanke hannu da ruwa da sabulu a kowani lokaci.
5. Zuwa asibiti da zaran an kamu da zazzabi ko idan ba a gane lafiyar jiki ba.