CUTAR DIPHTHERIA: Abubuwa 9 da ya kamata a sani game da cutar

Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta bayyana cewa mutum 123 sun kamu da cutar Diphtheria sannan cutar ta yi ajalin mutum 38 a jihohi hudu a kasar nan.

NCDC ta ce jihar Kano ce kan gaba a jerin jihohin da cutar ta ke yi wa illa. Sauran jihohin da cutar ta barke sun hada da Legas, Yobe da Osun.

Ga abubuwa 9 game da cutar Diphtheria

1. Menene cutar Diphtheria

Cutar Diphtheria cuta ce da kwayoyin cutar bacteria mai suna ‘Corynebacterium’ ke haddasa wa.

Cutar ya fi kama yara kananan da manyan mutane musamman wadanda ba su yi allurar rigakafin cutar ba.

2. Hanyoyin kamuwa da cutar.

Ana iya kamuwa da cutar idan ana yawan zama kusa da masu fama da cutar.

Idan mai dauke da cutar ya Yi tari ko atishawa ba tare da ya rufe bakinsa ba.

Sannan da yawan yin amfani da kayan da masu fama da cutar suka yi amfani da su kamar chokali, Kofi, hakichin da sauran su.

3. Mutanen da suka fi kamuwa da cutar

Cutar Diphtheria ya fi kama yara da manya musamman wadanda tun farko ba su Yi allurar rigakafin cutar suna yara ba sannan da kin yin allurar rigakafin yayin da suka girman.

4. Alamun cutar

Akan gane alamun cutar bayan ranar farko zuwa 10 da kamuwa da cutar.

Alamun cutar sun hada da zazzabi, yoyon hanci, ciwon makogwaron, idanun za su Yi jajawur, tari da Kumburin wuya.

Wasu lokuta mai fama da cutar zai Rika ganin wasu farin abubuwa na fitowa da a kusa da makogwaron sa wanda ke hana mutum iya yin numfashi da hadiyan abinci.

5. Abin da ke haddasa cutar

Kwayoyin cutar ‘Corynebacterium diphtheria’ ne ke haddasa cutar inda yakan kama hanci, makogwaron da fatara mutum.

6. Ire-iren cutar Diphtheria

Cutar diphtheria ya rabu biyu inda akwai ‘Classic respiratory’ wanda kan kama hanci makogwaro sannan da ‘Cutaneous’ wanda kan kama fatar mutum.

7. Hanyoyin gane cutar a jikin mutum

Jami’an asibiti na iya gano cutar daga alamun kamuwa da cutar da suka fara nunawa a jikin mutum kokuma idan aka Yi wa mutum gwajin cutar.

8. Maganin cutar

Wanda ya kamu da cutar zai killace kansa sannan maganin ‘Antibiotices’ na kawar da cutar daga jikin mutum.

Sannan ruwan dumi akai-akai na taimakawa wajen rage zafi da Kumburin makogwaro.

9. Hanyoyin guje wa kamuwa da cutar

A. Yin allurar rigakafi.

B. Saka takunkumin fuska musamman idan za a shiga cikin mutane.

C. Kare baki da hanci idan za a yi tari ko atishwa.

D. Tsaftace muhalli, wanke hannu da ruwa da sabulu a kowani lokaci.

E. Zuwa asibiti da zaran an kamu da zazzabi ko idan ba a gane lafiyar jiki ba