CUSHE: ICPC ta bankaɗo yadda aka maimata sunayen ayyuka 257 cikin Kasafin 2021

Shugaban Hukumar Yaƙi da Almundahana a Ma’aikatun Gwamnati (ICPC), Bolaji Owasanoye ya bayyana cewa ICPC ta bi diddigin kasafin kuɗi na 2021, inda ta gano akwai wuru-wurun maimanta sunayen ayyuka sau biyu har ayyuka 257 a cikin Kasafin Kuɗaɗe na 2021.

Bolaji ya ce ICPC ta gano wannan mummunar harƙalla ce bayan ta yi wa kasafin filla-filla.

Ya ce adadin kuɗaɗen da aka dafkara a cikin kasafin za su kai naira biliyan 20.138.

Bolaji ya zargi ma’aikatun da ministoci daban-daban ke jagoranta da kuma sauran hukumomin gwamnati da satar maƙudan kuɗaɗe ta hanyar cushe a cikin kasafin kuɗi, danƙara sunayen ma’aikatan bogi da kuma sauran laifukan zamba.

Bolaji ya ce a cikin kasafin 2021 wanda ke ƙarewa a shiga na 2022 aka gano wannan harƙalla da wuru-wuru.

Ma’aikatu da Bangaren Shugaba Muhammadu ne ke shirya kasafin shekara-shekara, sannan sai su tura wa Majalisar Dattawa da ta Tarayya. Bayan sun shigar da gyare-gyare ne zai a maida wa Shugaban Ƙasa ya sa wa kasafin hannu.

Yayin da a baya Majalisa ake zargi da cushe a kasafin kuɗaɗe. Amma a wannan karo ICPC ta fallasa ma’aikatun gwamnati ne.

Kasafin 2021: Majalisar Tarayya Za Ta Yi Bincike Kan Zargin Zambar Naira Biliyan 20 138

Majalisar Tarayya ta amince cewa kwamiti zai binciki zargin da ICPC ta yi cewa an yi cushen ayyuka 257 cikin kasafin 2021, waɗanda aka riƙa maimaitawa ce.

Adadin kuɗaɗen za su kai Naira biliyan 20.138 kamar yadda Shugaban Hukumar ICPC, Bolaji Owasanoye ya tabbatar.

Dan Majalisar Tarayya daga Jihar Filato, Dachung Bagos ne ya bayyana ya nemi a yi binciken, a zaman Majalisa na ranar Alhamis.

Shugaban Marasa Rinjaye, Ndudi Elumelu daga Jihar Delta ya nemi Kwamitin Kasafin Kuɗaɗe ya binciki zargin.

Sai dai Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila ya ce wannan zargi ai ƙusa ce mai inci tara Shugaban ICPC ya buga a kan Majalisar Tarayya, domin ita ce ta kafa kwamitin da ya tantance kasafin.

“Idan wannan zargi ya zama gaskiya, to bai kamata a maida wa kwamitin tantancewa wannan bincike ba. Saboda ya aka yi a baya su ka tantance, amma su ka kasa bankaɗo wannan zargi?

“Don haka sai dai a bai wa Kwamitin Musamman wannan aiki, ya yi wannan bincike.

Shi kuwa Ɗan Majalisa Tony Okechukwu, ya yi kira ne a binciki zargin an ɗaga wa Ofishin Shuagaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya ƙafa, aka amince ofishin ya ɗauki ma’aikata.