Cikin ‘ya’ya 10 da ake haihuwa wa magidantan Najeriya, 6 ba ‘ya’yan su bane kuma ba su sani ba – Likitan gwajin sanin kwayoyin halitta

Wani kwararren likitan gwajin asalin mahaifan ya’ya wato sanin kwayoyin halitta DNA Abiodun Salami ya bayyana cewa a cikin gwajin mata da mazaje 10 da ake yi wa gwajin sanin asalin kwayoyin halittar ya’yan su 6 daga ciki ana ganowa cewa ba ‘ya’yan su bane.

Masanin ya bayyana wani gwaji da suka yi akan wasu da ke jayayyar ‘ya’ya a tsakanin su da wata mata.

” Matar aure ce da mijinta suka haifi tagwaye. Daga baya wani tsohon saurayinta ya ce ‘ya’yan nashi ba na mijin ta bane. Haka aka yi ta kai ruwa rana har a yakai ga dole azo ayi gwajin jini. Dukkan su suka kawo samfurin su aka yi gwajin, amma kuma da sakamakon gwajin ya fito sai aka ga dukkan su biyu ma ba mahaifan wadannan tagwaye bane. wani can da ban da bai ma sani ba.

” Bayan haka mun rika samun mata da yawa suna zuwa a boye domin a yi musu gwajin da ‘ya’yan su kuma ana ganowa cewa ,mazajen da suke tare da su suka dawainiyar wadannan yaya ba sune mahaifan su ba. Matan suka boye hakan mazajen ba su sani har abada.

” Sannan kuma suma mazajen idan basu yarda da matar da suka aura ba, kai ko kuma ma sun yarda da su, a lokutta da yawa sukan garzayo suma a boye a yi musu gwajin sannan idan aka yi musu gwajin da dama sukan gano ashe ya;ayn da suka ta yi wa dawainiya ya’yan wasu ne ba na su ba.