CIKA-BAKIN APC A LEGAS: Guguwar komawar wani ɓangaren APC zuwa PDP ba zai haifar da komai ba

Jam’iyyar APC reshen Jihar Legas ta bayyana cewa har abada PDP ba za ta taɓa samun nasara a Jihar Legas ba.

Kakakin jam’iyyar na Legas, Seye Oladepo ne ya bayyana haka a ranar Asabar, biyo bayan komawar wani dandazon mambobin APC na jihar zuwa PDP.

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ne ya share wa mambobin waɗanda su ka ɓalle su ka raɗa wa kan su suna Lagos4Lagos hanyar shiga PDP.

Sai dai kuma APC ta ce ai jihar Legas kamar wutsiyar raƙumi ce, ta yi wa yaro nisa. Don haka duk wani ƙulle-ƙulle da munaficcin da wasu ‘yan cikin jam’iyya za su ɓalle su je cikin PDP su shirya, to ba zai sa PDP ta yi nasara ba a Jihar Legas.

“Ai in dai rashin nasara ce a kowane zaɓe a Jihar Legas, to a kullum a jinin PDP ya ke.

“Kuma ina tabbatar maku da cewa zaɓe mai zuwa haka PDP za ta lodi buhunan asara, don ko mazaɓa ɗaya ba za ta iya kashewa ba.” Inji Oladepo, Sakataren APC na Legas.

Jam’iyyar PDP dai har yau ba ta taɓa yin nasarar lashe zaɓen gwamna a jihar Legas ba, tun bayan dawowar mulkin dimokraɗiyya cikin 1999.

Bola Tinubu ne ya yi mulki tsawon shekaru takwas daga 1999 zuwa 2007, a ƙarƙashin AD. Sai kuma Raji Fasshola ya yi shekaru takwas, shi ma a ƙarƙashin AD, daga 2007 zuwa 2015.

Jam’iyyar APC ta riƙe daga 2015 har zuwa yau.