CANJIN SHEƘA: PDP ta nemi kotu ta tsige Gwamna Matawalle, Sanatocin Zamfara da ‘Yan Majalisu 27

Jam’iyyar PDP ta shigar da ƙarar neman kotu ta tsige Sanatocin Zamfara uku, ‘Yan Majalisa 27 tare da Gwamna Bello Matawalle, saboda canjin sheƙar da su ka yi ba bisa ƙa’ida ba, daga PDP zuwa APC.

PDP ta shigar da wannan ƙarar ta hannun babban lauya O.J. Onoja, wanda ya shaida wa Mai Shari’a Inyang Ekwo na Babbar Kotun Tarayya a Abuja neman tsige su, a cikin ƙara mai lamba FHC/ABJ/CD/650/2021, wadda ya shigar a ranar 30 Ga Satumba.

PDP na neman kotu ta tsige Gwamna Matawalle, Sanatoci uku, Mambobin Majalisar Tarayya shida tare da dukkan ‘yan Majalisar Jihar Zamfara, waɗanda su ka canja sheƙa daga PDP su ka koma APC.

Dama kuma PDP ta maka Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), APC, Shugaban Majalisar Dattawa da na Tarayya, Gwamna Matawalle da kuma Cif Jojin Jihar Zamfara ƙara, dangane da wannan dambarwa.

Matawalle da sauran sanatoci da mambobi da ‘yan Majalisar Jiha 24 sun koma APC a ranar 29 Ga Yuni.

Sai dai kuma an bar baya da ƙura, yayin da Mataimakin Gwamna, Mahdi Gusau bai sauya sheƙa ba.

Idan ba a manta ba, tun a ranar 8 Ga Yuli, PDP ta garzaya kotu, inda ta nemi a yi mata sharhin Dokokin Najeriya lamba 1(2), 188, 221, 177(c), 106(d) da kuma 65(2)(b) da ke cikin Kundin Tsarin Mulki na 1999.

Waɗannan dokoki dai su na magana ne a kan sauya sheƙa ga wanda aka zaɓa. To amma ita gwamnatin Bello Matawalle, ba zaɓen ta aka yi ba, APC ce Kotun Ƙoli ta haramta wa shiga zaɓe a jihar Zamfara. Don haka sai aka bai wa PDP nasarar.

Bayan hawan Matawalle a ƙarƙashin PDP, sai kuma duk su ka sauya sheƙa zuwa APC.

Yanzu dai an ɗage ci gaba da sauraren shari’ar zuwa ranar 2 Ga Nuwamba.