Buhari ya rantsar da sabon Cif Joji na riƙo

Shugaba Muhammadu Buhari ya rantsar da Olukayode Ariwoola a matsayin sabon Cif Jojin Najeriya na riƙo.
Rantsar da Ariwoola ya biyo bayan murabus ɗin da Tanko Muhammad ya yi ne, wanda a sanarwa aka ce ya ajiye aiki saboda yanayi na rashin lafiya.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa Tanko ya ajiye aikin sa mako ɗaya bayan Alƙalan Kotun Ƙoli ta Najeriya sun aika masa wasiƙar ƙorafin cewa ya fi su shan miyar dage-dade da jar miya.
An haifi Ariwoola ranar 22 Ga Agusta, 1958, a garin Iseyin da ke Jihar Oyo.
Kafin ya zama Alƙali a Kotun Ƙoli cikin 2011, ya yi alƙalanci a Kotun Ɗaukaka Ƙara daga 2005 zuwa 2011.
Wannan jarida ta buga labarin cewa Cif Jojin Najeriya ya yi murabus, mako ɗaya bayan alƙalan Kotun Ƙoli sun zarge shi da fin su shan dage-dage da jar miya.
A cikin labarin, Babban Jojin Najeriya Tanko Muhammad ya ajiye muƙamin sa, watanni 18 kafin lokacin ritayar sa.
Tanko dai kamata ya yi a ce zai yi ritaya a cikin Disamba 2023.
Sanarwa ta ce ya yi murabus ne saboda dalilai na rashin lafiya.
A cikin Disamba 2023 ne zai cika shekara 70 a duniya. Yayin da a yanzu shekarun sa 68.
Ba a dai bayyana irin rashin lafiyar sa ba.
Ana sa ran nan ba da daɗewa ba Shugaba Muhammadu Buhari zai rantsar da mafi girman muƙami daga cikin Alƙalan Kotun Ƙoli, wato Olukayode Ariwoola a matsayin Cif Joji na riƙo.
Tanko ya yi murabus ne mako ɗaya bayan wasu Alƙalan Babbar Kotun Ƙoli su 14 sun rubuta masa wasiƙar ƙorafin cewa ba ya jan su a jika, kuma ya fi su shan dage-dage da jar miya.
Acikin ƙorafin da su ka yi har da zargin ba ya kula da haƙƙoƙin su. Sannan kuma ya daina kashe kuɗi ana kunna janareton da ke bai wa Kotun Ƙoli wutar lantarki.
Alkalai 14 ne su ka sa wa wasiƙar ƙorafin hannu, wadda ta watsu kamar wutar-daji a soshiyal midiya.
An nada Tanko cikin 2019 kafin zaɓe, bayan Shugaba Buhari ya dakatar da Cif Joji Welter Onnoghen.