Buhari ya ce zai cika dukkan alƙawurran da ya ɗauka kafin a zaɓe shi

Shugaba Muhammadu Buhari ya sake ɗaukar wani sabon alƙawarin cewa zai cika dukkan alƙawurran da ya ɗauka kafin a zaɓe shi.

Ya yi alƙawarin cewa zai cika alƙawurran kafin cikar wa’adin zangon sa na biyu a cikin watan Mayu, 2023.

Duk da irin gagarimin rikice-rikicen da ya tirniƙe a faɗin ƙasar nan, Buhari ya ce hakan ba zai hana shi cika dukkan alƙawarin da ya ɗauka ba.

PREMIUM TIMES ta yi cikakken nazarin yadda gwamnatin Buhari ta ƙasa magance matsalar tsaro da matsalar tattalin arziki.

Sannan kuma Buhari wanda ya taɓa yin shugabanci a zamanin mulkin soja, yanzu da ya ke mulki a tsawon shekaru shida na mulkin dimokradiyya, ya kasa tsaida tattalin arzikin kasar nan bisa turba sahihiya.

Sannan kuma yaƙi da cin hanci da rashawa na ɗaya daga cikin alƙawurran da ya yi wa ‘yan Najeriya a lokacin da ya ke roƙon su jefa masa ƙuri’a.

Buhari ya sake yin wannan alƙawarin a ranar Juma’a, lokacin da ‘yan ƙungiyar Muhammadu Buhari and Osinbajo su ka kai masa ziyasa a Fadar Shugaban Ƙasa.

Ƙungiyar ta kai ziyarar ce domin damƙa wa Buhari kundin adadin dukkan ayyukan da Gwamnatin Buhari ta samar a ƙasar nan, daga 2015 zuwa 2020.

“Wannan ƙungiya ta MBO Dynamic Support Group ta ga irin ayyukan alherin da mu ka yi daga lokacin da mu ka hau mulki zuwa 2020.”

Ya gode wa ƙungiyar tare da cewa kundin zai zama matattarar ayyukan da gwamnatin sa ta aiwatar.

Sannan kuma ya gode wa ƙungiyar bisa wannan gagarimin tattara ayyuka da ta yi.

Littafin dai kamar yadda Shugaban Ƙungiyar, Usman Ibrahim ya bayyana, ya ƙunshi shafukan 295.