Buhari a nada sabbin shugabannin hukumar gudanarwar Kamfanin mai na kasa, NNPC

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada shugabannin hukumar gudanarwar kamfanin mai na kasa, NNPC.

Sanarwar wanda mai ba shugaban Kasa shawara kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya fitar ranar Lahadi ya bayyana Sanata Ifeanyi Ararume shugaban kwamitin gudanarwar kamfanin mai din.

Ga sunayen:

Senator Ifeanyi Ararume – Shugaban hukumar gudanarwar
Mele Kolo Kyari da Umar I. Ajiya, shugaba da mai kula da harkokin kudi

Sauran sun hada da Dr Tajudeen Umar (Arewa Maso Gabas), Mrs Lami O. Ahmed (Arewa Ta Tsakiya), Mallam Mohammed Lawal (Arewa Maso Yamma), Senator Margaret Chuba Okadigbo (Kudu Maso Gabas), Barrister Constance Harry Marshal (Kudu Maso Guduh), da Chief Pius Akinyelure (Kudu Maso Yamma).

Shugaba Muhammadu Buhari, a matsayinsa na Ministan harkokin man fetur ya bayar da umarnin mayar da kamfanin mai na NNPC a matsayin wanda zai iya ba da dama a zuba hannun jari, wato Nigerian National Petroleum Company Limited.

Wannan ya yi dai-dai da bangare na 53(1) na Dokar Man Fetur ta 2021, wadda ta bukaci Ministan Man Fetur ya mayar da kamfanin wanda za a iya zuba jari cikin wata shidda bayan sa hannu kan dokar.

Don haka ne Shugaba Buhari ya bukaci shugaban kamfanin, Malam Mele Kolo Kyari, ya dauki matakan da suka dace don tabbatar da sauya kamfanin.