BINCIKEN ‘ Pandora Papers’ Rayuwar Walter Wagbatsoma, ƙasurgumin mazambaci, abokin ‘cin mushen’ tsohuwar minista Diezani

Daga cikin gaggan ɓarayin da su ka jidi kuɗaɗen Najeriya su na harƙalla a ƙasashen waje, sunan wani makusancin tsohuwar ministar fetur, Diezani Allison-Maduekwe da ake kira Walter Wagbatsoma bai fito fili ba sosai. Amma ɓarnar da ya yi ko ambaliyar ruwan sama sai haƙa.

A ranar 17 Ga Fabrairu, 2018 an ɗaure Wagbatsoma shekaru 6 a Ingila, kuma aka haramta masa zama daraktan wani kamfani.

Kafin kotu ta ɗaure shi, sai da aka fara kulle shi tsawon shekaru uku da watanni shida saboda an haɗa baki da shi aka yi damfarar karkatar da fam miliyan 13 mallakin hukumomin gwamnatin Birtaniya, ciki kuwa har da haƙƙin kuɗaɗen Hukumar Tara Kuɗaɗen Tallafin Masu Taɓin Hankali ta Lincolnshire (NHS).

Kafin sannan, a cikin watan Yuni 2016 an taɓa tsare shi a Birtaniya, daidai lokacin da ya ke komawa daga wata tafiya da ya yi ƙasar Jamus.

Kotun Leicester ta hukunta Wagbatsoma bisa samun sa da laifin amfana da fam 480,000 daga hukumomin gwamnati huɗu.

An samu Wagbatsoma da wasu abokan daƙa-daƙar sa sun damfari asibitoci, majalisu, makarantu da ƙungiyoyin samar da gidaje.

Bayan su Wagbatsoma sun kai ga kuɗin, sun roƙi a tura masu kuɗaɗen ta wani asusun ajiya daban, bisa ƙaryar cewa na su asusun ajiyar ya na da matsala.

Bayan an tura masu kuɗaɗen inda su ke nemi a tura, sai aka riƙa tut-tura kuɗaɗen daga wannan aausu zuwa wancan, don kawai a kasa gano yadda su ka yi da kuɗaɗen.

Jami’an ‘Yan Sandan Lincolnshire sun shafe shekaru huɗu su na binciken su Wagbatsoma, waɗanda wani gungu ne na ƙasurgumai kuma tantiran ‘yan iskan ‘yan damfara.

Cikin 2011 aka fara binciken harƙallar su Wagbatsoma, bayan sun damfari Lincolnshire Partnership NHS Trust fam miliyan 1.28.

Wagbatsoma: Ɓarawo A Najeriya, Ɓarawo A Birtaniya:

A lokacin da ake tuhumar Wagbatsoma a Birtaniya, nan a Najeriya ma ana wata shari’ar sa a kan zargin danne kuɗaɗen tallafin fetur.

Wagbatsoma hamshaƙin ɗan hada-hada ne, kuma babban dillalin fetur ne daga ƙasashen Turai.

An tabbatar cewa Wagbatsoma ya fi kowa kusancin shirya daƙa-daƙa shi da tsohuwar ministar fetur, Diezani Allison-Madueke.

Wagbatsoma ya yi aiki da kamfanin Shell tsakanin 1991 zuwa 1993. Daga nan ya koma aiki a Zenith Bank tsakanin 1993 zuwa 2001.

Tsakanin 2001 zuwa 2003 ya yi aiki da FSB International Bank Plc. Daga nan kuma sai ya ɓulla kamfanin Ontario Oil and Gas, a matsayin Mataimakin Shugaban Kamfani.

Wagbatsoma ya kafa kamfanonin karkatar da maƙudan kuɗaɗe a Seychelles da British Virgin Islands.

Wagbatsoma Da Harƙallar Kuɗaɗen Tallafin Fetur:

A ranar 12 Ga Agusta, 2012 ne EFCC ta gurfanar da Wagbatsoma Babbar Kotun Lagos, bisa zargin da hannun sa a harƙallar tallafin fetur.

An zarge shi tare da abokan harƙallar sa da laifin kantara karya don a karɓi kuɗi, damalmala lissafin kuɗi, yin fojare na buga kwafen takardu da kuma haɗa baki domin a yi zamba.

Cikin 2017, bayan an shafe shekaru biyar ana tafka shari’a, Mai Shari’a Lateefa Okunnu ta Babbar Kotun Jihar Legas ta ɗaure shi tsawon shekaru 10 a kurkuku.

A daidai lokacin da aka yi masa wancan ɗaurin shekaru 10 a Najeriya, can a Birtaniya kuma Wagbatsoma ya na fuskantar tuhumar zambar fam miliyan 12.