BINCIKEN ‘Pandora Papers’: An bankaɗo yadda tsohon gwamnan Kano da wasu tsoffin gwamnoni 20 su ka ɓoye Naira biliyan 117 a ƙasar waje

Sun kwashe kuɗaɗen sun bar ‘yan garin su da jihohin su da al’ummar su cikin ƙuncin rayuwa. Daidai lokacin da Hukumar Ƙididdigar Alƙaluman Bayanai ta Ƙasa (NBS) ta bayyana cewa a duk cikin mutum 10 a Najeriya, guda 4 ba su da abincin yau ballantana na gobe. Kuma a wasu jihohin ma mutum 9 a cikin 10 ke halin kame-kamen rufin asiri, saboda abin da su ke samu a rana bai kai Naira 377 ba.

To a wannan lokacin ne kuma Pandora Papers ta bankaɗo wani tsohon ministan Najeriya da Gwamnoni 21 su ka bi ta hannun manajojin Trident Trust Company (BVI) Limited su ka kimshe dala miliyan 100 da fam na Ingila miliyan 77.3 na kuɗaɗe da kadarori a Standard Chartered Bank na garin Guernsey a Jersey da kuma Burtaniya.

Akwai kuma wasu madarar kuɗaɗe dala 511, 860 da fam 50,000 duk a Standard Bank su kuma a Jersey ɗin.

A kan yadda Babban Bankin Najeriya (CBN) ke bayar da canjin kuɗi kan dala Naira 410, fam na Ingila kuma Naira 588, waɗannan zunzurutun kuɗaɗe za su iya kai Naira biliyan 84.

Amma a kasuwar ‘yan canji kuɗaɗen za su kai Naira biliyan 117, idan aka canja dala a kan kan Naira 575, fam na Ingila kuma kan Naira 775.

Waɗannan ‘yan Najeriya su 35 na daga cikin jami’an gwamnati fiye da 300 da kuma biliniyoyi sama 130 daga ƙasashe daban-daban na duniya.

‘Yan Najeriya ɗin da aka lissafa akwai tsoffin gwamnoni, tsohon minista da kuma wasu hamshaƙan attajirai.

Dokar Najeriya dai ba ta hana kai kuɗi kasashen waje domin yin halastaccen kasuwanci, matuƙar hada-hadar halas ce za a yi, kuma kuɗin idan ba na sata ba ne.

Amma an yi ittifaƙi cewa su na kimshewa waje ne domin kauce wa biyan haraji da kuma aikata muggan ayyukan laifuka.

Su na amfani da wasu kamfanonin waje ne can su ba su amanar kuɗaɗen a rubuce bisa sharuɗɗa masu tsauri.

Akwai masu ɓoye kuɗaɗe a waje saboda taɓarɓarewar tattalin arzikin Najeriya, sai kuma hawa da sauka na farashin dala da kuma wasu tsare-tsaren gwamnati waɗanda ba ta iya samar da nagartaccen tsarin tattalin arziki.

Wasu kuma na ganin cewa harajin da gwamnatin tarayya ke tsulawa ya yi yawa matuƙa. Shi ya sa ba su iya zuba jarin su a nan Najeriya.

Matsalar Da Kimshe Kuɗaɗen Najeriya A Ƙasashen Waje Ke Haifarwa:

Yayin da ake kwasar kuɗin da aka karkatar daga Najeriya zuwa ƙasashen waje, Naira ce ke rage daraja. Haka wani masanin tattalin arziki da ke Stanbic IBTC, mai suna Femi Owolabi ya shaida wa PREMIUM TIMES.

Tsakanin 2006 zuwa 2015, an karkatar da dala biliyan 8.3 daga ƙasashe 39, ciki har da Najeriya, kamar yadda Global Financial Integrity (GFI) ya buga rahoton sa a cikin 2019.

Wata ƙungiyar Binciken Ƙwaƙwaf ta Amurka mai suna IFF, ta sanar da cewa Najeriya rasa kuɗaɗen shiga har dala biliyan 157 tsakanin 2003 zuwa 2012.

Waɗannan maƙudan kuɗaɗe da su ka mallaka ya nuna irin bambanci da ratar da ke tsakanin hamshaƙan ‘yan Najeriya da kuma faƙirai masu fama da rayuwar ƙunci.

Cikin makon da ya gabata dai Hukumar Tara Kuɗaɗen Haraji ta Ƙasa (FIRS) ta ce za ta bi masu ɓoye kuɗaɗen a ƙasashen waje da Pandora Papers ta fallasa domin ƙwato harajin shekara da shekaru da su ka kauce wa biya:

Ga Sunayen Su Nan A Ƙasa:

1. Sani Bello, Tsohon Gwamnan Kano:

Wannan dattijo da a yanzu ya kai shekaru 78 a duniya, hamshaƙin attajiri ne. Cikin 2012 Mujallar Forbes ta bayyana Sani Bello na 38 a cikin Manyan Attajiran Afrika 40.

Forbes ta ƙiyasta cewa Sani Bello ya na da tsabar kuɗi da kadarorin da sun kai dala miliyan 500, kwatankwacin Naira Biliyan 287.5.

Shi ke da kamfanin Sandel Holdings Limited, inds ya ɓoye naira biliyan 22.9 a ƙarƙashin Bankin Standard Chartered Bank, a Guernsey.