Bankin IMF zai taimaka wa Najeriya da shawarwarin fasaha da tsare-tsare – eNaira

Bankin Bada Lamuni na Duniya (IMF) ya bayyana cewa a shirye ya ke ya taimaka wa Najeriya da shawarwarin fasaha da tsare-tsare, domin ta samu nasarar shirin eNaira.

IMF ta yi wannan ƙudiri a cikin wata sanarwa da Sashen IMF Mai Kula da Afrika ya fitar a ranar Talata.

IMF ta lura cewa ganin yadda cukumurɗa da girman tattalin arzikin Najeriya ya ke, tsarin eNaira da ta ƙaddamar cikin watan Oktoba, ya fara jan hankalin ƙasashen duniya da Manyan Bankunan Ƙasashe.

Kamar sauran tsarin kuɗin dijital, shi ma tsarin eNaira ya na tattare da kasada sannan kuma akwai sauran ƙalubale da kuma alfanun ƙarfafa tattalin arziki.

Cikin watan jiya ne Bankin CBN ya buga Naira Miliyan 500, ya raba wa bankuna Naira Miliyan 200.

Najeriya ta buga sabbin kuɗin eNaira miliyan 500, kuma ta raba wa bankunan kasuwanci eNaira na miliyan 200.

Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele ne ya bayyana haka a lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da sabuwar hada-hadar zamani ta eNaira, ranar Litinin a Abuja.

Emefiele ya ce tuni har manyan bankuna da hamshaƙan masu hada-hada da sauran dubban jama’a sun yi wa tsarin tun a lokacin da ake ƙaddamar da shi kai-tsaye.

Ya ce tuni har bankuna 33 sun shiga sahun hada-hadar kai-tsaye a cikin tsarin manhajar, kuma sama da gaggan ‘yan hada-hada 120 su ka samu nasarar yin rajista a tsarin na eNaira. Kuma sama da kwastomomi 2000 ne su ka shiga.

“A yau duk kwastomomin da su ka shiga cikin manhajar eNaira za su iya yin abubuwan da su ka haɗa da:

“Za su iya buɗe na su alaben, za su iya zuba wa alaben su na eNaira daga asusun su na ajiya a banki, za su iya tura kuɗi daga alaben su na eNaira zuwa alaben wani abokin hulɗar su na eNaira. Kuma za su iya saye ko sayarwa ko biyan kuɗi daga alaben su.”

Emefiele ya jinjina wa Shugaba Buhari, inda ya ce ya kafa gagarimin tarihi, wanda ƙaddamar da eNaira a Najeriya shi ne na farko a Afrika.

Cikin watan Satumba, Bankin CBN ya ce bai ƙirƙiro hada-hadar eNaira don ya ƙwace wa bankuna kwastomomi ba.

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya kwantar wa ɗaukacin bankunan kasuwanci na Najeriya rai, yayin da ya bayyana cewa bai ƙirƙiro tsarin hada-hadar kuɗaɗe na eNaira don ya ƙwace wa bankunan kwastomomin su ba.

Ya ce tsarin an fito da shi ne domin bayar da damar hada-hada ga ba’arin mutanen da ba su samun damar shiga wasu hada-hadar kuɗaɗe.

CBN ya bayyana haka a ranar Litinin, yayin da ya ke ƙarin haske a sabon shafin eNaira na yanar gizo.

A ranar 1 Ga Oktoba ne dai CBN zai ƙaddamar da fara aiki da amfani da tsarin na eNaira.

Ya ce shiri ne na bunƙasa sabon tsarin kasuwanci ta intanet domin cibiyoyin hada-hadar kuɗaɗe su ƙara samun kwastomomin da ke yawan ƙara wa kuɗaɗen ajiyar su na banki nauyi.

CBN ya bayar da bayani dalla-dalla kan yadda tsarin eNaira zai shafi ɗaiɗaikun jama’a, ‘yan kasuwa, gwamnati da ƙungiyoyin da ba na gwamnati ba.

“Cibiyoyin Hada-hadar Kuɗaɗe sun kasance wani tsani ko gada tsakanin kwastomomi da Bankin CBN. Wannan tsari zai taimaka wajen ƙarfafa hada-hadar su.

“Tsarin eNaira ba wata dabara ba ce da CBN ya fito da ita domin ƙwace wa bankunan kasuwanci kwastomomin su.”

Tsarin eNaira na da alaƙa da haɗa dukkan kwastomomin da ke amfani da tsarin da kuma lambar asusun ajiyar kuɗaɗen su a banki.

“Sannan kuma a ƙarƙashin tsarin akwai adadin da kwastoma zai iya hada-hadantarwa, domin kada ya riƙa saurin kwashe kuɗaɗen sa, ya na haddasa wa cibiyoyin hada-hadar kuɗaɗe tabka asara.

“ENaira zai matuƙar rage ayyukan ‘yan damfara sosai, harƙalla da kuma daƙile masu ƙoƙarin karkatar da kuɗaɗe, saboda akwai lambar ‘code’ da za a iya bin diddigin kowace eNaira.”

Makonni uku da su ka gabata CBN ya ce tilas kowa ya karɓi e-Naira a hada-hadar sa.

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana cewa sabuwar ƙwandalar ‘dijital’ ta e-Naira da za a fito da ita, za kasance wani kuɗin Hada-hadar da za a riƙa amfani da shi baya ga Naira, kamar yadda dokar ƙasa ta amince da shi.

Babban Bankin Najeriya ne ya bayyana haka ta bakin Daraktan Tsare-tsaren Biyan Kuɗaɗe na CBN, Musa Jimoh ya bayyana a ranar Litinin.

Ya yi wannan ƙarin haske ne a lokacin da gidan talabijin na Channels ke tattaunawa da shi a ranar Litinin.

“A yau duk inda ka miƙa naira tilas a karɓa a matsayin ta na takardar kuɗin da dokar Najeriya ta amince a yi hada-hada da ita. To haka abin ya ke da wannan sabuwar ƙwandalar e-Naira da za a fito da ita a ranar 1 Ga Oktoba, 2021. Duk wanda aka bai wa e-Naira tilas ya karɓa.” Inji Jimoh.

A ranar 30 Ga Agusta ne CBN ya bayyana fito da e-Naira daga ranar 1 Ga Oktoba.

Za a fito da ita ce domin ta maye gurbin ‘cryptocurrency’ a ƙasar nan, bayan da CBN ɗin ya haramta, tun a cikin watan Fabrairu.

E-Naira dai ba wasu ƙwandaloli ne za a riƙa yawo da su a cikin aljihu ba. Hada-hadar kuɗaɗe ce ta intanet.

Dalili kenan ma CBN ya yi kira ga duk mai wayar sadarwa samfurin Android ko iPhone cewa su kwashi manhajar e-Naira wallet a daga rumbun kwasar manhajojin ‘application stores’ a wayoyin su.

Da aka tambaye shi anya Najeriya ta shirya bin wannan tsari kuwa, domin ana ganin za a iya fuskantar matsaloli a tsarin hada-hadar e-Naira.

Amma sai ya ce ba ya tsammanin wannan tsari ya na da wahalar da zai iya kawo wani cikas ko matsala a ƙasar nan.

“Ai ba cewa aka yi rana ɗaya kowa tilas ya karɓe ta ba, ko ya yi mu’amala da ita ba. Abin zai ɗan ɗauki lokaci, kafin ya karaɗe ko’ina na sassan ƙasar nan da kuma kowane irin hada-hadar kasuwanci.”

“Idan ka tuna a baya akwai lokacin da a ƙasar nan ba kowa ke yarda da tsarin POS ba. Amma yanzu kuma ya cika ko’ina.”

A ƙarshe ya wani ƙarin alfanun e-Naira shi ne za a rage buga takardun kuɗaɗe, kuma za a rage yawan jigilar kuɗaɗe daga nan zuwa can.