BANKA WA HEDIKWATAR APC WUTA: Shekarau, Barau Jibrin sun aika wa Sufeto Janar da ƙorafi

Tsohon Gwamnan Kano kuma Sanata Ibrahim Shekarau da Sanata Barau Jibrin da kuma Sha’aban Sharaɗa, sun rubuta wa Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Alƙali Usman wasiƙa mai ɗauke da ƙorafin banka wa Ofishin APC na Sanata Barau Jibrin wuta da wasu ‘yan daba su ka yi.

Wasiƙar wadda aka rubuta a ranar 2 Ga Disamba, ta na ɗauke har da sa hannun sauran Ɗan Majalisar Tarayya Nasiru Abduwa da kuma Tijjani Joɓe da Haruna Dederi.

Su shida duk sun danganta kai wa ofishin jam’iyyar da hukuncin da Kotun Tarayya ta bayar a Abuja, inda ta rushe tare da haramta zaɓen shugabannin jam’iyya na ɓangaren Ganduje, wanda aka ce shugaban jam’iyyar da ke kai, Abdullahi Abbas ne ya lashe.

Kotu ta haramta zaɓen su Abdullahi Abbas, daga jihar har zuwa matakin ƙananan hukumomi.

Kuna ta gargaɗe su cewa kada su kuskura su sake zaɓen shugabannin. Domin kotun ta amince da shugabancin ɓangaren su Shekarau, waɗanda su ka zaɓi Haruna Ɗanzago.

PREMIUM TIMES HAUSA ta bada labarin banka wa ofishin wuta kuma ta buga labarin yadda ‘yan sanda su ka kama mutum 13 da ake zargi na da hannu.

Takardar Ƙorafi Ga Sufeto Janar:

A cikin wasiƙar ƙorafin, su Shekarau sun zargi Abdullahi Abbas da alhakin ɗaukar nauyin waɗanda su ka banka wutar.

Cikin waɗanda aka zarga kuma har har da Kwamishinan Lura da Ƙananan Hukumomi, Murtala Garo, Faizu Alfindiki, wanda shi ne Shugaban Ƙaramar Hukumar da ya jagoranci rusa wani ginin koya wa matasa sana’o’i da Sha’aban Sharaɗa ya fara yi.

Sai kuma Khalid Diso Shugaban Ƙaramar Hukumar Gwale, Hassan Garban Ƙauye na Ƙaramar Hukumar Kumbotso, sai kuma Shugaban Ƙaramar Hukumar Nasarawa.

Yayin da su ka yi kira ga Sufeto Janar da ya ɗauki matakin binciken gaggawa, sun kuma yi gargaɗin cewa idan wani abu ya same su ko magoya bayan su, to waɗannan da su ka ambata ne ke da hannu.

Sai dai kuma kakaki waɗanda aka zarga ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa sharri ne aka yi masu.

Ahmed Aruwa ya ce su ma tashi su ka yi da safe su ka ji labarin an banka wutar. “Amma ba waɗanda aka lissafa cikin zargin ba ne su ka ɗauki nauyin ‘yan dabar.” Inji Aruwa.