Ban cika son shirya bukin murnar zagayowar ranar haihuwa ta ba -Atiku a shakaru 75

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar ya bayyana cewa shi kwata-kwata ba mutum ba ne mai son shirya bukin murnar zagayowar ranar haihuwar sa ba.

Atiku ya bayyana haka a garin Bauchi, inda ya buɗe wani sabon titi mai tsawon kilomita 4.2, da ke bai-fas na kan hanyar Gombe Road zuwa Maiduguri Road, wanda aka raɗa masa sunan Atiku Abubakar.

Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi ne ya raɗa wa titin sunan Atiku, kuma ya gayyace shi buɗe titin.

“To a yau na karanta bayanai masu ratsa jiki na gaishe-gaishen taya ni murnar cika shekaru 75 a duniya. Duk da ni mutum ne da ba ya bukin murnar zagayowar ranar haihuwar sa, sai ga shi a nan kun kawo min kek na taya ni murna, tare da ƙaton bijimin sa.

“To ni dai ban taɓa yin irin haka ba. Kuma ba a taɓa yi min irin haka ba.

“Mai girma gwamna na yi matuƙar farin cikin da ba ni ma iya bayyana irin daɗin da na ji a yau.

“Ina roƙon al’ummar jihar Bauchi su ci gaba da goyon bayan gwamnan su. Saboda babu abin da ya fi buƙata kamar goyon bayan ku, domin zai fi jin daɗin yi maku ayyukan raya ƙasa da inganta al’umma.”

Haka nan Atiku ya gode wa Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, wadda ya ce duk da ‘yan adawa ke da rinjaye a cikin ta, ba su yi wa gwamna tarnaƙi da dabaibayin hana shi yin aiki ba.

Ya Atiku ya gode wa Gwamna Bala bisa karimci na gayyatar da ya yi domin buɗe ayyuka a Jihar Bauchi.

Ya ce ya ƙara shaƙuwa ba Bala tun ya na Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja.