Bamu kori kowa gwamnatin Kaduna ba maimakon haka ma kara ma’aikata muka yi – In ji El-Rufai

Gwamna Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa har yanzu gwamnatin sa bata kori kowa daga aiki a jihar Kaduna ba, maimakon haka ma kara daukar ma’aikata gwamnati ta yi.

A hira da yayi da gidajen radiyo dake jihar Kaduna, gwamna El-Rufai ya ce gwamnatin sa bata kori kowa daga aiki a jihar ba.

” Idan kuka duba yadda muke biyan albashi a jihar, za ku ga a cikin watanni biyu da suka wuce maimakon aka yawan ma’aikata na raguwa, karuwa suke yi. Babban dalilin haka kuwa shine mun kara daukan ma’aikata ne maimakon zargin mu da wasu ke yi wai miuna rage ma’aikata.

” Mun dauki sabbin ma’aikata a jami’ar KASU, haka kuma mun kara yawan yawan ma’aikata da asibitocin mu, ga shi kuma zamu dauki malaman makarantun sakandaren jihar har 7000.

El-Rufai ya ce wadanda za a zaftare daga aikin ba wasu bane illa wadanda gwamnati bata bukatar su.

” Gwamnati na tantance irin wadannan ma’aikata. Wasu daga cikin wadanda ke aiki a gwamnatin jihar ba su da takardun kirki. Wasu ma takardun wasu suke amfani da shi, wasu kuma ma na karya ne, wasu ma gaba daya basu da takardun ma a haka suke aiki kuma ake biyan su. Irin su ne za mu bi day bayan daya mu zaftare su.

Gwamna El-Rufai ya ce shi ba shi da burin rage albashi kamar yadda wasu jihohin kasar nan ke yi. Ya ce maimakon haka kara albashi yake da burin yi da zaran gwamnati ta samu karin kudin shiga.