Ba za mu bari a yi zanga-zangar tuna ranar fara Tarzomar #EndSARS ba -Ƴan Sandan Legas

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Legas Hakeem Odumosu, ya gargaɗi masu neman shirya zanga-zanga cewa ba za su bari a gudanar da zanga-zangar tunawa zagayowar ranar fara Tarzomar #EndSARS ba.

Cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun Kakakin Yaɗa Labaran ‘Yan Sandan Jihar Legas, Adekunle Ajesebutu, Hakeem ya ce “Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Legas ba za ta bari masu zanga-zanga su sake jefa al’ummar Jihar Legas cikin irin mummunan halin da su ka jefa ta a lokacin Tarzomar #EndSARS a 2020 ba.”

An dai gudanar da zanga-zangar, wadda ta rikiɗe zuwa ƙazamar tarzoma daga ranakun 8 zuwa 20 Ga Oktoba, a Lagos.

“Tarzomar #EndSARS ta jefa jama’a cikin mummunan tashin hankali. Miliyoyin mazauna Legas sun ɗanɗana halin ƙunci, rasa rayukan ɗimbin jama’a, sai kuma asarar ɗimbin dukiyoyin gwamnati da na sauran jama’a masu tarin yawa.”

Idan ba a manta ba, Gwamnatin Najeriya ta zargi mai Tiwita da laifin daukar nauyin kuɗaɗen shirya zanga-zangar #EndSARS.

Ministan Yaɗa Labarai Lai Mohammed ya bayyana cewa kamfanin Tiwita ya yi ladab, ya nemi zaman sulhuntawa da sasantawa da Gwamnatin Najeriya.

Lai Mohammed ya bayyana wa manema labarai na Fadar Shugaban Kasa halin da ake ciki tun bayan dakatar da Tiwita daga Najeriya.

Lai ya yi karin hasken ne bayan tashi daga Taron Majalisar Zartaswa tare da Shugaba Buhari a ranar Laraba.

Ministan ya kara jaddada cewa an karya fukafikin ‘yar tsuntsuwar Tiwita a Najeriya, saboda sun bayar da kofa ga wasu marasa kishin kasa su na amfani da kafar da nufin wargaza Najeriya.

Lai ya ce Shugaban Tiwita ne ya rika daukar nauyin dukkan kudaden da masu shirya tarzomar #EndSARS su ka kashe a lokacin zanga-zangar.

“Sannan kuma Tiwita ta bai wa Shugaban IPOB damar watsa sanarwar mambobin IPOB su rika kashe jami’an tsaro, kuma su rika banka wa kadarorin gwamnati wuta.”

Lai ya ce duk da Gwamnatin Najeriya ta yi ta rokon Tiwita cewa ta cire sanarwar Nnamdi Kanu da ya yi shelar a fara kisan ‘yan sanda ana banka wa kadarorin gwamnati wuta, Tiwita ta yi kunnen-uwar-shegu da kiraye-kirayen.

Daga ya lissafa sharuddan da ya ce tilas sai Tiwita ta cika kuma ta amince da su, kafin a amince ta ci gaba da aiki a Najeriya.