BA A RABU DA BUKAR BA: Rikicin haƙƙin mallakar kuɗaɗen harajin VAT da wasu jihohi bai hana Gwamnatin Tarayya mafarkin tara naira tiriliyan 2.2 a shekarar 2022 ba

Gwamnatin Tarayya ta fara mafarkin ganin ta tara naira tiriliyan 2.26 daga Harajin Jiki Magayi (VAT) a cikin shekara mai zuwa ta 2022.

Sannan kuma ta na da ran shigar kuɗaɗe har Naira tiriliyan 10.5 daga ɓangarori daban-daban a cikin asusun Gwamnantin Tarayya.

Wanann hasashen dai ya na cikin Hasashen Tsare-tsaren Kuɗaɗen Shiga na shekarun 2022-2024.

Wannan hasashe ya zo a daidai lokacin da Gwamnatin Tarayya ke cikin tsaka-mai-wuya, inda wasu gwamnoni su ka ce sun daina bari Gwmnatin Tarayya na karɓar harajin VAT a jihohin su.

Tuni dai Jihar Ribas ta hana Gwmnatin Tarayya karɓar VAT a can, inda yanzu haka ana kotu, bayan gwamnatin tarayya ɗin ta ɗaukaka ƙarar hukuncin da Babbar Kotun Tarayya a Jihar Ribas ta yanke cewa jihar ce ke da haƙƙin karɓar VAT ba Gwamnantin Tarayya ba.

Tuni dai jihohin Legas da Ribas su ka kafa dokokin karɓar harajin VAT da kan su, tare da haramta wa Gwamnatin Tarayya karɓar VAT ɗin a jihohin su.

Hukumar Tara Harajin Cikin Gida, wato Federal Inland Revenue Services (FIRS) ke karɓar VAT a madadin Gwamnatin Tarayya.

Sannan kuma dukkan kudu sun yi taro kwanan nan a Enugu, inda su ka nuna goyon bayan hana Gwamnatin Tarayya karɓar
VAT da jihohin Ribas da Legas su ka yi.

Sai dai kuma duk wannan bai hana gwamnatin tarayya mafarkin tara kuɗaɗen harajin VAT har naira tiriliyan 2.26 a 2022 ba.

Ba a kan batun Harajin VAT ne kaɗai jihohi ke sa-in-sa da Gwamnatin Tarayya ba.

Kwanan baya Gwamnoni 36 sun maka Gwamnatin Buhari kotu, bisa zargin yi masu rinton kuɗaɗen haraji Naira biliyan 176.

Gwamnonin Najeriya 36 sun sake maka Gwamnantin Shugaba Muhammadu Buhari ƙara a Kotun Ƙoli, inda su ke neman kotu ta tilasta wa Gwamnatin Tarayya ta maida masu kuɗaɗen harajin naira biliyan 176 da Gwamnatin Tarayya ta karɓa a hannun mutane a faɗin jihohin ƙasar nan.

Maƙudan kuɗaɗen da ake tankiya a kan su ɗin dai Gwamnatin Tarayya ta karɓe su ne tsakanin 2015 zuwa 2020 a jihohin Najeriya, da sunan ‘Harajin Stamp Duties’.

Harajin ‘Stamp Duties’ dai wasu kuɗaɗe ne da Gwamnatin Tarayya ke tatsa a jikin kowane ɗan Najeriya, a duk jihar da ya ke idan ya ciri kuɗi a asusun sa na banki, ko kuma ya tura kuɗi a wani asusu daga asusun ta, ko ta waya, ko ta POS ko ta na’urar ATM ko kuma kai-tsaye daga cikin banki.

Waɗannan kuɗaɗen ne jihohin Najeriya su ka ce kowace jiha ke da haƙƙin karɓar su a jihar ta, ba haƙƙin gwamnatin tarayya ba ne karɓar kuɗaɗen.

Bisa wannan dalili ne kowane Antoni Janar na jihohi 36 ya shigar da ƙara a madadin jihar sa a Kotun Ƙoli. Kuma kowace jiha ta ɗauki lauyan ta, inda su ke neman Gwamnatin Tarayya ta maido masu jimlar Naira biliyan 176 da ta tatsa a cikin jihohin ƙasar nan daga 2015 har zuwa ƙarshen 2020.

Wannan dambarwa ta taso a daidai lokacin da Babbar Kotun Tarayya ta Fatakwal ta haramta wa Gwamnatin Tarayya karɓar Harajin VAT a Jihar Ribas, inda kotun ta ce harajin VAT haƙƙin gwamnatin jiha ne, ba na gwamnatin tarayya ba ne.

Tuni ita ma jihar Legas har Majalisar Dokokin ta sun kafa dokar daina biyan VAT ga Gwamnatin Tarayya a Jihar Legas, sai dai a riƙa biya ga gwamnatin jiha.

Haka kuma wanann dambarwa ta zo ne wata ɗaya bayan Gwamnatocin Jihohi 36 sun kafsa jayayya da Gwamnatin Tarayya kan batun biyan wasu ‘yan gidoga Naira biliyan 171 daga asusun jihohi da ƙananan hukumomi.

Gwmnatocin Jihohi 36 sun shigar da ƙarar neman a biya su kuɗin harajin Stamp Duties a ranar 24 Ga Agusta, a Kotun Ƙoli.

PREMIUM TIMES ta ga kwafen shigar da ƙarar, mai lamba SCN/CV/690/2021.

PREMIUM TIMES Hausa ta buga wancan labarin gidoga dalla-dalla.