Ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan Ta’adda shirme ne ba zai yi tasiri ba – Gumi

Fitaccen malamin addinin musulunci dake Kaduna, Sheikh Ahmed Gumi ya soki ayyana ‘yan bindiga da kotu ta yi a matsayin ‘yan ta’adda cewa shirme kuma ba zai yi tasiri ba.

Idan ba a manta ba Kotu ta ayyana ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda kamar yadda a abaya ta ayyana kungiyar IPOB a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda.

“Shawarar da gwamnati ta yanke ba za ta yi wani amfani a aikace ba, domin tun kafin sanarwar ana yaki da su ana daukarsu a matsayin ‘yan ta’adda.

“Idan za a iya tunawa, IPOB ita ma an bayyana kungiyar ta ‘yan ta’adda, har ma da umurnin kotu ya goyi bayan haka, amma ko kasashen duniya ba su amince da ayyana kungiyar ta IPOB ‘yan ta’adda ba.

” Ga ‘yan IPOB dinnan har yanzu suna cin karen su babu babbaka, Su fita zuwa kasashen waje daga najeriya babu abinda ake musu duk da ayyana su a matsayin ‘yan bindiga da akayi, babau tasirin da abin yayi sai bata wa mutane lokaci kawai da aka yi.

” Ina fatan ‘yan Najeriya ba za su dauki ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda ba, wasu tsiraru daga cikin su na aikata ta’addanci kamar yadda ‘yan IPOB ke yi aikata akan musamman ‘yan Arewa.

” Babu abin da zai canja, sojoji na can suna yaki da su amma kullum jiya iyau, sace-sacen mutane ne aka daina ko kuma kashe mutane? Babu ko daya saboda haka kiran su ‘yan ta’adda kawai bata yawun baki ne gwamnati ta yi.

” Fulani sun sha wuya a kasar nan, an sace musu shanu da sauransu an kwace musu dukiyoyin su har da hadin bakin jami’an tsaro duk aka wulakan ta su. dole a jawo su a jiki a inganta su suma.