AREWA A HANNUN ‘YAN BINDIGA: Kotu ta ayyana cewa masu garkuwa da ‘yan bindiga su ma ‘yan ta’adda ne

Babbar Kotun Tarayya ta ayyana ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane cewa su ma ‘yan ta’adda ne, kamar Boko Haram da ISWAP.

Wadda hukunci ya ƙarfafa kiraye-kirayen da jama’a su ka riƙa yi wa gwamnatin tarayya cewa ta ɗauki ‘yan bindiga da ‘yan Boko Haram duk matsayi ɗaya, ‘yan ta’adda ne gaba ɗayan su.

Daraktan Gurfanar da Masu Laifi a Kotu na Tarayya (DPP) Mohammed Abubakar ne ya shigar da muradin neman kotu ta ayyana su matsayin ‘yan ta’adda.

An shafe shekaru 10 ‘yan bindiga na addabar wasu yankuna na Arewacin ƙasar nan. Har ta kai abin kusan ya zama bala’i a yankunan Arewa maso Yamma baki ɗaya.

Da ya ke gabatar da muradin, Abubakar ya shaida wa kotu cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannun amincewa da ayyana ‘yan bindiga matsayin ‘yan ta’adda.

Da ya ke zartas da hukunci, Mai Shari’a Taiwo Taiwo, ya ce munanan ayyukan da ‘yan bindiga da masu garkuwa ke yi cewa ta’addanci ne ƙarara.

Takardun bayanan da ke gaban kotu sun nuna cewa gwamnatin tarayya ta ayyana ‘yan bindiga matsayin ‘yan ta’adda, saboda a na kashe mutane, garkuwa da mutane, banka wa garuruwan da ƙauyuka wuta da kuma yi wa mata da ‘yan mata fyaɗe.

“Gwamnatin Tarayya ta ƙara kafa hujja da yadda su ke garkuwa da ƙananan yara, musamman ɗaliban sakandare da na Islamiyya, satar shanu, bautar da mutane, ɗaure mutane, ƙuntata wa waɗanda su ka kama, tsare mata su na lalata da su tsawon lokaci, ɗirka wa matan mutane da ‘yan mata ciki, hare-hare da lalata kayan gona da sauran dukiyoyin jama’a.”