AREWA A HANNUN ‘YAN BINDIGA: Hotunan wasu gwamnonin Arewa tare da abokin gogarma Turji sun tayar da ƙura a Arewa

Masu tofa albarkacin bakin su a soshiyal midiya na buƙatar a yi binciken dangantakar da ke tsakanin wasu gwamnoni da gogarman ‘yan bindiga Bello Turji, bayan ɓullar wasu hotuna da kuma bayanan da suka fito daga bakin wani makusancin Turji ɗin da aka kama.

Cikin hotunan an ga Musa Karmanawa abokin Turji tare da gwamnonin Zamfara da na Sokoto, wato Bello Matawalle da Aminu Masari da kuma Mataimakin Gwamnan Sokoto, Mannir Ɗan’iya.

An kama Karmanawa cikin shekarar da ta gabata a Abuja, tare da wani mutumin Jamhuriyar Nijar, mai suna Bashar Audu, tare da buhunan wiwi da za a kai wa Bello Turji.

An kama Karmanawa tun cikin watan Satumba, 2021, amma bidiyon tambayoyin da aka yi masa ya ɓulla a soshiyal midiya ne kwanan nan.

Mugu Shi Ya San Makwantar Mugu: Dangantakar Karmanawa Da Turji:

Musa Karmanawa ya ce shi da Turji abokai ne na ƙut da ƙut, kuma su na bai wa juna shawara a kan hare-hare ko farmakin da su kan yi.

A tambayoyin da ake yi masa, ya ce aƙalla akwai dakarun ‘yan bindiga kamar 100 da a koyaushe ke kewaye da Bello Turji, su na tsaron lafiyar sa.

Haka nan kuma ya bayyana sunayen masu kai wa Turji makamai da kayan sojoji da na ‘yan sanda da makamai da kuma sauran kayan buƙatu na yau da kullum.

Albasa Ba Ta Yi Halin Ruwa Ba: Dangantakar Karmanawa Da Bafarawa:

Musa Karmanawa ɗan uwa ne ga tsohon Gwamnan Jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa, wanda a ko yaushe ya ke fitowa kafafen yaɗa labarai ya na neman gwamnati ta ƙara masa lambar kakkaɓe ‘yan bindiga.

Attahiru Bafarawa ƙani ne ga mahaifiyar Musa Karmanawa.

Musa Karmanawa wanda ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Isa ne, ya na da cikakkiyar masaniyar dazukan yankin Sokoto ta Gabas da Zamfara ta Arewa, musamman ƙauyukan da su ka yi iyaka da Shinkafi a Zamfara da kuma Isa a Sokoto.

Binciken da PREMIUM TIMES ta yi, ta gano cewa Karmanawa na daga cikin waɗanda Gwamnatin Bello Matawalle ta fara tuntuɓa cikin 2019 bayan ya hau mulki, domin ya shiga tsakani a sasanta da ‘yan bindiga.

Wata majiya a Gidan Gwamnatin Zamfara, wanda kuma Mashawarcin gwamna ne, ya shaida wa Premium Times cewa an tuntuɓi Karmanawa ne bayan an ƙirƙiro batun neman sasantawar.

“Duk da Bello Turji a lokacin bai amince da karɓar tayin sasantawar ba, amma dai ɓangarorin ‘yan bindiga da dama sun amince, kuma sun miƙa makaman su ta hannun mai shiga tsakani, Musa Karmanawa.

“A lokacin mu ba mu san ya na tare da su ba, kuma ba mu san ya na yi masu aiki ba. Ashe dalili kenan da ya ke yawan ce mana mu ƙara faɗaɗa tattaunawar neman sulhu da ‘yan bindiga.

“Kowa zai shaida cewa a lokacin ya yi sanadiyyar karɓo tulin bindigogin da aka kawo nan Gusau. Kuma a gaskiya an samu zaman lafiya a lokacin.

Haka wani jami’in gwamnati ya shaida wa wakilin mu, amma ya roƙi kada a bayyana sunan sa.

Sai dai kuma ya kasa tabbatarwa shin ko wasiƙar da ke ɗauke da sanarwar naɗa Karmanawa Mai Taimakawa Na Musamman Ga Gwamna, shin ta gaske ce ko ta bogi ce ba.

“Ni dai ban ga wasiƙar ba. Shin idan ma gaskiya ne an naɗa shi, to na tabbatar Matawalle ya yi hakan ne da kyakkyawar niyya, domin gudunmawar shi Musa Karmanawa ɗin wajen karɓo makamai daga hannun ‘yan bindiga da kuma zaman lafiyar da aka samu a lokacin.

Musa Karmanawa: Goga Abokin Gwamnati, Gazagurun Abokin Turji:

Wannan jarida ta gano cewa Musa Karmanawa ne gwamnati ta damƙa wa mahaifin Bello Turji, shi kuma ya kai masa shi har bakin ƙorama, a lokacin da Bello Turji ya ce ba zai saki waɗansu mutum 50 da ya kama ba, sai an saki mahaifin sa da aka kama a Jigawa, kan hanyar sa ta zuwa wani gari, tunda shi ba ɗan bindiga ba ne.

Cikin bidiyon da Premium Times ta saurara a cikin watan Yulin 2021, an ji Bello Turji ne cewa:

“Wallahi idan za a bai wa Musa Karmanawa mahaifi na ya kawo min shi bakin ƙorama, to ni ma zan kai masa waɗanda na ke tsare da su ɗin a bakin ƙorama.”

PREMIUM TIMES Hausa ta buga cikakken labarin a lokacin.

Wani malami a Jami’ar Sokoto ya ce Karmanawa ba ƙaramin ɗan ta’adda ba ne. Ya kamata a matsa bincike domin a fallasa duk wani babba mai ɗauke m wa matsalar tsaro gindi.

Shi kuwa wani malamin addinin musulunci mai suna Murtala Assada, cewa ya yi bai ga dalilin da zai sa a tsare Karmanawa a bar sauran iyayen gidan sa da ke cikin gwamnati ba.

Ya ce Karmanawa ai ɗan aiken Turji-Turjin da ke cikin gwamnati ne a birni, zuwa ga Bello Turji da ke cikin daji.

Kakakin Yaɗa Labaran Gwamnan Zamfara, Zailani Bappa ya ce shi bai ga wani abin tada ƙura ba don an nuno hoton Matawalle da Karmanawa tare.
.ya ce an yi hoton ne tun lokacin da aka yi zaman sulhu.

Shi ma Kakakin Yaɗa Labaran Gwamnan Sokoto, ya ce hoton Tambuwal tare da Karmanawa a Gidan Gwamnatin Sokoto da ke Abuja aka yi shi.

“Kuma a lokacin za ta yiwu ya je ne kawai a matsayin sa na mai ziyara, kamar yadda sauran ‘yan jihar Sokoto kan kai, idan Gwamna ya shiga babban Birnin Tarayya.