AREWA A HANNUN ‘YAN BINDIGA: An tura jami’an tsaro garin da mahara su ka aika wasiƙar sanarwar kai masu hari a Sokoto

Rundunar ‘Yan Sanda a Jihar Sokoto ta tura jami’an ta a garuruwan da ‘yan bindiga su ka aika wa shirin kwana da sauraren zuwa kai masu hari.

PREMIUM TIMES ta buga cewa wasu ‘yan bindiga sun aika wasiƙa, wadda su ka rubuta da Hausa, wadda a cikin ta su ka bayyana shirin kai ga yankunan da su ka aika wa wasiƙun.

Cikin wasiƙar, ‘yan bindiga sun ce, “idan mazauna yankin sun ga dama, su kira sojoji sama da 100 don su kare su, amma wannan ba zai hana su ‘yan bindigar su kai masu hari ba.”

Ƙauyukan da aka aika wa wasiƙun sun haɗa da Kwanar Kimba, Shuni, Dange da Rikina.

Wata majiya a cikin garin Isa, mai suna Basharu Altine, ya bayyana wa wakilin mu cewa ana zaman ɗar-ɗar a yankunan, tun bayan da ‘yan bindiga su ka raba masu wasiƙu.

“Wasu na ganin cewa wasiƙun kamar na bogi ne kawai. Su na tunanin wasu ‘yan iskan yara ne kawai su ka rubuta wasiƙun. To amma a gaskiya dai ba mu so maharan nan su shammace mu, domin za su iya komai.” Inji Altine.

Ya ce wasu matasa ne su ka tsinci wasiƙar a Kwanar Kimba, a ranar Asabar.

Kakakin Yaɗa Labarai na ‘Yan Sandan Sokoto, Sanusi Abubakar, ya shaida wa wakilin mu cewa sun ɗauki wannan wasiƙa da gaske ce kawai, shi ya sa ma su ka gaggauta ɗaukar matakan tsaro a yankunan.

Ya ce an ƙara tura zaratan jami’an tsaro a yankunan da maharan su ka yi wa barazanar kai masu farmakin.