APCn KANO TA DAGULE: Ba za mu halarci taron gangamin APCn Kano ba – Shekarau, Jibrin

Jam’iyyar APC a jihar Kano ta faɗa cikin tsaka mai wuya, bayan wasu jiga-jigan jam’iyyar, Sanata Ibrahim Shekarau, Sanata Barau Jibrin da wasu ƴan majalisar dake wakiltar jihar Kano a majalisar Tarayyar sun zargi gwamnan jihar Abdullahi Ganduje da yin gaban kansa ga al’amuran jam’iyyar ba tare da tuntuɓar su ba.

Ƴan majalisan sun wanda suka yi taron gaggawa a Abuja sun aikawa shugaban jam’iyyar na kasa, Mala Buni wasikar sanin matsayin su game da halin da jam’iyyar ke ciki a jihar Kano.

A cikin wasikar, sun koka kan yadda gwamnan jihar tare da makarraban sa a jigar suke yin gaban kan su ba tare da yin shawara da kowa ba.

” Kowa ya san irin gudunmawar da muka bada a zaɓen 2019. Amma bayan an gama zaɓen shi kenan aka wancakalar da mu. Ganduje ya kama gaban sa, sai yadda ya so ya ke yi da APC a Kano. Ba ya neman mu ballantana wai har yayi shawara da mu game da wani abu da ya shafi jam’iyyar.

” Jam’iyyar Karkashin Ganduje ta ki cika alkawuran da ta ɗauka bayan nasara a zaɓe da aka yi a 2019. Wasu tsiraru ne ke tafiyar da harkukin jam’iyyar, kuma suna yin yadda suka ga dama ne abinsu ba tare da tuntuɓar ƴaƴan jam’iyyar ba.

” Saboda haka ba za mu amince da kokarin gudanar da zaben jam’iyyar na jihar Kano da ake shirin yi a karshen mako ba. Ba mu tare da waɗanda suka shirya zaben da kuma gwamnati akan haka.

Sai dai kuma shugaban Jam’iyyar Abddullahi Abbas ya ce kuturu yayi kaɗan, domin jam’oyyar ta kammala shiri tsaf don gudanar da zaben Kano.

” Ba kuma za mu matsar da zaben ba.” In ji Abbas