APC TA DAGULE A KANO: APCn Shekarau ta zaɓi Zago, ta Ganduje kuma Abbas

Bangaren su tsohon gwamnan jihar Ibrahim Shekarau, sun zaɓi Ahmadu Danzago a matsayin shugaban jamiyyar APC a jihar.

Duk da cewa jami’an tsaro sun hana ɓangaren Shekarau gudanar da zaɓen bayannsun taru a wajen yin zaɓen bayan haka sun yi zaɓen a Janguza da ke ƙaramar hukumar Tofa.

A ɓangaren gwamnan Ganduje kuma sun zaɓi Ɗan sarki Abdullahi Abbas a matsayin shugaban APC na Kano.

Duka shugabannin biyu sun rattaba hannun a takardar amincewa su shugabanci jam’iyyar.

Yanzu dai APCn Kano ta daɗa dagulewa domin karshenta kuto za ta raba gaddama tsakanin bangarorin biyu.

Sai dai kuma wanda jam’iyyar APC ta tura Kano domin kula da zaɓen, Farfesa Mohammed Bello ya ce an gudanar da zaɓe lafiya, kuma shugaban da ɓangaren sanata Shekarau suka zaɓa ne sabon shugaba APC.