ANA WATA GA WATA: CBN ya ƙara kuɗin ruwa zuwa kashi 16.5% kafin fito da sabbin kuɗi

Yayin da ake cikin zaman zullumi da taraddadin halin da za a iya shiga sakamakon sauya launin kuɗi, Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ƙara kuɗin ruwa ga masu karɓar ramcen kuɗaɗe zuwa kashi 16.5%.
Bankin ya ce yin hakan zai rage tsada da hauhawar farashi, kuma zai rage matsin da ake yi wa naira har ana ƙoƙarin takure ta a jikin bango.
Gwamnan CBN Godwin Emefiele ne ya bayyana sanarwar wannan ƙari a ƙarshen zaman Kwamitin Tsare-tsaren Hada-hadar Kuɗaɗe (MPC), wanda ya gudana ranar Talata, a Abuja.
CBN ya ce tuni aka fara ganin alfanun ƙarin kuɗin ruwan da aka yi a baya, don haka akwai buƙatar a ci gaba da riƙe akalar gam-gam.
Emefiele ya ce kwamitin bai ƙara adadin Kuɗaɗen Ajiyar Bankuna a CBN ba, wato ‘Cash Reserve Ratio’ (CRR).
Waɗannan kuwa wasu adadin kuɗaɗe ne da CBN ta gindaya wa bankuna za su riƙa ajiyewa a CBN ɗin, daga cikin kadarori da kuɗaɗen da masu ajiya ke ajiyewa a bankunan. CBN ya ce har yanzu adadin ya na nan a kashi 32.5%.
Cikin Oktoba dai malejin tsadar rayuwa ya cilla sama zuwa kashi 21.09%, tashin da bai taɓa yin irin haka a baya ba, tsawon shekaru 17.
Wani ƙalubalen da CBN ke fuskanta kuma shi ne yadda zai rage yawan kuɗaɗen da ke hannun jama’a, a lokacin da farashin kayan abinci da na masarufi su ka yi tashin gwauron zabo.
A ƙoƙarin da CBN ke yi don rage yawan kuɗaɗen da ke hannun jama’a, bankin ya yi sanarwar sauya launin Naira 200, 500 da 1,000. A cikin Disamba sabbin kuɗaɗen zasu fara shiga hannun jama’a.
Yanzu dai darajar dala 1 na daidai da naira 775 a kasuwar ‘yan canji, ba kamar yadda ta ke naira 790 a ranar Juma’a. Amma a farashin gwamnati ana sayar da dala 1 kan naira 445.38 ga mai hanya ko kuma mai rabo.