Ana Ci Gaba Da Samun Sakamako Na Bazata A Qatar: Japan Ta Ba Jamus Mamaki Da Ci 2-1

Kwallayen da Ritsu Doan da Takuma Asano suka ci bayan da suka shigo wasa cikin minti 15 na karshe, sun bai wa Japan damar bada mamaki inda ta yi wa Jamus mai rike da kofi har sau hudu ci 2-1 a gasar cin kofin duniya da suka buga ranar Laraba.