An sako Sarkin Bunguɗu, bayan ya shafe kwanaki 32 a hannun Ƴan bindiga

‘Yan bindiga sun saki Sarki Bunguɗu Hassan Attahiru, bayan ya shafe kwanaki 32 tsare cikin daji a hannun su.

An kama shi ne tsakanin Kaduna zuwa Abuja, a tsakiyar watan Satumba.

PREMIUM TIMES ta bada labarin kama shi tare da ɗan sanda dogarin sa, bayan an bindige jami’in tsaron sa ɗaya.

Sanarwar da ta fito daga Fadar Masarautar Bunguɗu a Jihar Zamfara, ta ce sarkin ya na Kaduna ya na hutawa tare da iyalan sa.

Sai dai kuma sanarwar ba ta ce an biya kuɗin fansa ko ba a biya ba, kafin a sake shi.

Sanarwar ta gode wa Gwamnatin Jihar Zamfara, Gwamnatin Jihar Kaduna, Rundunar ‘Yan Sanda da kuma Ƙungiyar Makiyaya Fulani ta Miyetti Allah (MACBAN) bisa ƙoƙarin su wajen kuɓutar da Sarkin, wanda kuma shi ne ke riƙe da Sarautar Sarkin Fulanin Bunguɗu.

Cikin makon jiya PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda Sarkin Bunguɗu ya shafe kwanaki 30 a hannun masu garkuwa bayan an biya kuɗin fansa, amma har yau babu labarin sa.

Har yau iyalai, abokai da fadawan Sarkin Bunguɗu, Hassan Attahiru ba su san halin da ya ke ciki ba, kwanaki 30 bayan kama shi da yin garkuwa da shi.

‘Yan bindiga sun kama shi a kan hanyar Abuja daga Kaduna, inda bayan sun bindige ɗan sandan da ke kare lafiyar sa, sun kuma haɗa da wani ɗan sanda ɗaya tare da Sarkin, duk su ka nausa cikin daji da su.

Lamarin ya faru a ranar 14 Ga Satumba, wanda tun bayan nan ba a sake jin ɗuriyar sa ba.

Sarkin Bunguɗu wanda ake wa lakabi na Sarautar Sarkin Fulanin Bunguɗu, tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa ne.

Sakataren Masarautar Bunguɗu Muhammadu Usman, ya shaida wa BBC Hausa cewa a baya dai wasu makusantan Sarki da ke wajen Zamfara sun riƙa magana da masu garkuwar, inda su ka yi ƙoƙarin karɓo shi.

Ya ce amma saboda matsalar kulle layukan waya, a yanzu ba su da labarin halin da Sarkin ya ke ciki.

Wata majiya a Fadar Sarkin Bunguɗu da ba ta so PREMIUM TIMES ta ambaci sunan ta, ta ce “yanzu haka ba mu san halin da ya ke ciki ba. Ko ya na da rai, ko babu. Amma dai mu na da yaƙini a ran mu cewa ya na da rai.

“A baya an tattauna, har an kai kuɗin fansa. Amma kuma daga nan ba mu ƙara jin wani bayani ba, ko muryar sa ba a sake ji ba. Bayan kuma sun ce za su sake shi.”

Idan ba a manta ba, ranar 15 Ga Maris, an yi garkuwa da Sarkin Bukkuyum shi ma na Jihar Zamfara, bayan an yi musayar wuta da jami’an tsaron sa.

Sai dai kuma an sake shi bayan sati ɗaya da kama shi.