An kashe babban Kwamandan Boko Haram (ISWAP) Albarnawi

Rahotanni daga jihar Borno sun ce an kashe shugabann ƙungiyar ISWAP Abu Musab Al-Barnawi.

Rahotannin masu karo da juna na nuna cewa sojoji ne suka kashe shi, yayin da wasu majiyoyi kuma ke cewa a rikicin cikin gida ya mutu, RFI ta ruwaito.

Ya zuwa wannan lokaci rundinar soji bata sanar da kashe shugaban na ƙungiyar ISWAP ba a hukumance.

Shidai Al-Barnawi ɗa ne ga Muhammad Yusuf, mutumin da ya kafa ƙungiyar Boko hHaram kafin jami’an tsaro su kashe shi a shekarar 2009 lokacin da ya ƙaddamar da yaƙi akan su, abinda yayi sanadiyar mutuwar aƙalla mutane sama da dubu guɗa a lokacin.

A shekarar 2016 kungiyar ISWAP ta sanar da naɗa Al Barnawi a matsayin jagoran ta wanda kafin nan Abubakar Shekau ne ke jagoranci.

Kafin sauƙe Shekau daga jagorancin ƙungiyar ya bayyana goyan bayan sa ga ƙungiyar IS a watan Maris na shekarar 2015, tare da kashe dubban mutane sakamakon kai hare hare a garuruwa daban daban da jikkata mutane da kuma lalata kadarori da dama.

  • An kashe babban Kwamandan Boko Haram (ISWAP) Albarnawi
  • Da Ɗumi-Ɗumi: Ƴan bindiga sun sace Sarkin Bungudu na jihar Zamfara

Kawar da shi daga jagorancin ƙungiyar a shekarar 2016 ya bada damar naɗa Al Barnawi a matsayin sabon jagora da kuma raba mayaƙan ƙungiyar zuwa gida biyu.

Jaridar Daily Trust tace an naɗa Al Barnawi ya jagoranci ƙungiyar a Yankin Tafkin Chadi ne saboda hukunta Shekau wanda ya sabawa dokokin ta da kuma ci gaba da samun goyan bayan mayaƙan ƙungiyar da suke tare da manufofin mahaifin sa Muhammad Yusuf.

Jaridar tace rahotanni sun ce ƙungiyar ISIS ce ta horar da Al Barnawi kafin ya zama shugaban ISWAP, yayin da ya ƙaddamar da zafafan hare hare, ciki har da waɗanda suke kaiwa sansanonin soji a Yankin Tafkin Chadi, yayin da ya ƙaddamar da manufofin kawar da tasirin Shekau.

Bayanai sun ce Al Barnawi ya mallaki yanki mai girma a Arewacin jihar Borno, inda ya sanya haraji akan mazauna wurin, yake kuma tara kudi sosai daga aikin kamun kifi, bayan taimakon da yake samu daga ƙungiyar ISIS.

An wallafa wannan Labari September 15, 2021 8:38 AM