An kama waɗanda suka kashe ɗan Sanata Na’Allah da motarsa da suka sace a Nijar

An kama mutum biyu daga cikin waɗanda ake zargi da kashe matashin matukin jirgin saman nan, Kyaftin Abdulkareem, babban ɗan Sanata Bala Ibn Na’Allah.

Rahotanni sun ce an kama mutanen ne kwanaki kaɗan da kisan matashin mai shekara 36 a gidansa dake garin Kaduna aka kuma yi awon gaba da motarsa.

Da yake tabbatar da kama wadanda ake zargin, Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar Ƴan Sanda Jihar Kaduna, ASP Jalige Mohammed, ya ce, “Gaskiya ne mutum biyu daga cikin waɗanda ake zargi sun kashe Abdulkareem Na’Allah suna hannunmu. Daya kuma ya tsere”.

  • An kama waɗanda suka kashe ɗan Sanata Na’Allah da motarsa da suka sace a Nijar
  • An miƙa rahoton binciken dalilin hatsarin jirgin Janar Ibrahim Attahiru

Babu cikakken bayani game da waɗanda ake zargin da suka shiga hannu, amma majiyarmu ta ce matasa ne masu shekara 20 da wani abu.

Majiyar ta ce an kuma gano motar mamacin, wadda maharan da suka kashe shi suka yi awon gaba da ita a kan iyakar Jamhuriyar Nijar. Majiyarmu ta Aminiya ta ruwaito.

A ranar 29 ga watan Agusta ne aka yi wa matashin matuƙin jirgin saman kisan gilla a gidansa da ke unguwar Malali GRA a garin Kaduna.

Mahaifin Abdulkareem dai shi ne Sanata mai wakiltar Kebbi da Kudu a Majalisar Dattawa.

An wallafa wannan Labari September 16, 2021 11:25 AM