An kama mutane 21 da ake zargi da yin kisa da maita a Adamawa

Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da cafke mutane 21 da ake zargi da hannu a kisan mutane bakwai, wadanda ake zargin ta hanyar maita, a wani ƙauye a Adamawa.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Aliyu Adamu, a wani taron manema labarai a ranar Litinin a Yola, ya tabbatar da kama waɗanda ake zargi daga ƙauyen Dasin Bwate, dake ƙaramar hukumar Fufore a jihar.
Kamfanin Dillacin Labaru na NAN ya ruwaito Kwamishinan ya ce a halin yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, amma yankin kura ya lafa a yankin a halin yanzu.

An kama mutane 21 da ake zargi da yin kisa da maita a Adamawa
Yadda wasu matasa suka kashe ƴan bindiga 13 a ofishin ƴan sanda a Sokoto

Adamu ya ce kamen, da kuma sauran nasarori da hukumar ta samu, ya faru ne sakamakon kyakkyawar alaƙar aiki dake tsakanin rundunar da sauran hukumomi, mafarauta da ƴan banga, da kuma yadda ‘yan sanda ke yin tsayin daka a yaƙi da rashawa.
A cewar Kwamishinan, rundunar ta kuma yi nasarar tarwatsa tare da cafke bata gari da ake kira “Shilla Boys” sama da 400, waɗanda ke addabar mutane a Yola da kewayenta, kuma an gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu.
Kazalika ya ce sun kama sama da masu garkuwa da mutane 126 a fadin jihar tare da kubutar da waɗanda aka sace da dama.

Tura Wa Abokai

An wallafa wannan Labari September 20, 2021 4:10 PM