AN GUDU NA A TSIRA BA: Ƴan bindiga sun yi garkuwa da mutane 11 a Shimfiɗa, jihar Katsina

Tun bayan cire sojoji daga makarantar Sakandare da ke Shimfiɗa mutanen yankin suka fara arcewa daga wannan ƙauye saboda tsoron kada ayi garkuwa da su.

Sai dai kuma wasu daga cikin masu gudun sun faɗa hannun ƴan bindiga a lokacin da suke kokarin arcewa zuwa garin Jibia.

Wani mazaunin garin Abdurrazak Ahmad ya ce masu gudun na kokarin shiga sansanin ƴan gudun hijira ne dake garin jibia sai suka faɗa hannun ƴan bindiga suka yi awon gaba da su.

” Dama sojoji dake makarantar sakandare na gwamnatin dake Shimfida ne suka hana ƴan bindiga shigowa cikin garin Shimfida. Tun da aka cire su shi kenan sai ƴan bindigan suka samu daman shigowa garin.