Amina Muhammad ta sake zama mataimakiyar Sakatare Janar na MDD

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Sakataren Janar na Majalisar ɗinkin duniya (MDD) Antonio Guterres ya sake naɗa Ambasada Amina Muhammad a matsayin mataimakiyar sa a karo na biyu.

Hakan ya biyo bayan sake amincewa da naɗashi sakataren Majalisar da Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi a karo na biyu don sake jan ragamar majalisar na tsawon shekaru biyar wanda wa’adi na biyun zai fara aiki daga 1 ga watan Janairun 2022.

Amina, wadda tsohuwar Ministar Muhalli ce a mulkin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari na farko, Guterres ya naɗata mataimakiyarsa a shekarar 2017 bayan ya karbi ragamar Majalisar Ɗinkin Duniya daga hannun Ban Ki-Moon.