AMBALIYAR QATAR 2022: Spain ta kori kociya Luis Enrique bayan ta kwashi buhun kunya a hannun Marocco

Hukumar Ƙwallon Ƙafar Spain (SFF) ta kori mai horar da ‘yan wasan ta, Lius Enrique a ranar Alhamis.

Wata sanarwa ta bayyana cewa Shugaban Hukumar Luis Rubiales, ya cire Luis Enrique, ya maye gurbin sa da Lius de la Fuente.

Kafin naɗin da aka yi wa De la Fuente, shi ne mai horas da ‘yan ƙasa da shekaru 21 na ‘yan wasan Spain.

Sanarwar ta gode wa Enrique bisa ƙoƙarin sa tsawon shekaru huɗu ya na koyar da ‘yan wasan Spain.

Spain ta huce haushin ta kan kociya Enrique ne bayan ta sha kashi a wasan zagaye na biyu, a hannun Maroko da ci 3:0 a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Enrique shi ne kociya na huɗu da Spain ta kora daga 2028.

SFF ta ce a yanzu abin da ta sa a gaba shi ne ganin ta sake gagarimin shirin lashe kofin Turai wanda za a yi a Spain ɗin nan gaba.

Sabon kociyan dai ya samu shiga koyar da ‘yan ƙasa da shekaru 15 na Spain a 2013, kuma shi ne ya ƙyaƙƙyashe ‘yan Wasa irin su Marco Assensio, mai tsaron gida Unai Simon, Eric Garcia, Dani Olmo da sauran su.

Idan za a tuna, a lokacin da Spain ta sha kashi a hannun Maroko, Enrique ya shaida wa ‘yan jarida cewa ya ɗauki alhakin abin kunyar da Spain ta yi.

A gefe ɗaya dama ana ta sukar kociyan, ganin yadda ya cika ƙungiyar da ‘yan wasan Barcelona.

An yi mamakin yadda ya ƙi ɗaukar Sergio Ramos da Lucas Verquez.