Allah yayi wa limamin masallacin Maiduguri Road, Dahiru Lawal-Abubakar rasuwa

Allah yayi wa babban limamin masallacin Maiduguri Road dake Kaduna Sheikh Dahiru Lawal Abubakar rasuwa.
Lawal-Abubakar ya rasu ranar Laraba, a asibitin sojoji na 44 bayan jinya da yayi da ɗan wani lokaci.
Dahiru Lawal-Abubakar ya rasu yana da shekaru 52 kuma shine babban Alƙalin kotun shari’a dake Makarfi jihar Kaduna.
Da ya ke tabbatar da rasuwar Sheikh Lawal-Abubakar, ɗaya daga cikin ƙannen sa, tsohon editan Daily Trust kuma mawallafin jaridar Darlteline, Nasir Lawal-Abubakar ya ce ” Mun yi rashin yaya, makwafin mahaifin mu. Muna rokon Allah ya gafarta masa Amin.
Allah ya ji ƙan sa ya sa Aljannah ta zamo makoma.