Al-Nasrr Ta Musanya Vincent Abubakar Da Cristiano Ronaldo

A labaran wasanni na daren yau, akwai batun Cristiano Ronaldo, da na Karim Benzema da na Marcus Rashford, da kuma batun klub na Super Eagles.

Saidai da farko za a ji cewa kungiyar kwallon kafa ta Al Nassr, ta kasar Saudiyya ta ce wa dan kasar Kamaru Vincent Abubakar da ya san inda dare ya masa, inda ta musanya shi da shahararren dan kwallon duniya, Cristiano Ronaldo, kamar yadda kafar labarai ta Al-Riyad ta kasar Saudiyya ta labarto cewa yanzu dai Vincent Abubakar yana Free Transfer ne ga mai so, Vincent Abubakar dai ya ciwo kwallaye guda goma sha uku wa klub din Al-Nassar, yakuma taimaka wajen ciwo kwallaye guda shida, ana alakanta shi da klub din Manchester United na kasar Ingila.

A wata sabuwa kuma, Cristiano Ronaldo, ya sayar da kofin Ballon d’Or da ya samu a shekarar 2013 ma wani fitaccen mai kudi na kasar Isira’ila, mai suna Idan Ofer, kan kudi fam na Ingila Dubu dari biyar da talatin da biyu. Shi dai Ronaldo sau biyar yake samun kyautar kofin dan wasan kwallon kafa na duniya

Dan wasan gaba na klub din Manchester United Marcus Rashford, klub din Real Madrid, ta zabe shi a matsayin wanda zai maye gurbin Karim Benzema. A halin da ake ciki dai Karim Benzema yana karshen watanni shida na kwantaraginsa da klub din Real Madrid, kuma zai iya barin klub din kadaran kada hakan, Kamar yadda kafar El Nacional ta ruwaito, Benzema ba dan wasa kamar yadda yake a da ba sabili da yawan rauni da yake samu.

Tsohon dan wasan kwallon kafa na Najeriya Daniel Amokachi, ya ce matsalar kungiyoyin kwallon kafa na kasa, suna da alaka da  yadda hukumar kwallon kafa ta kasa, NFF ta ke daukar kococin da ba su cancanta ba, da kuma gayyatar, ‘yan wasan da basu dace ba. Daniel Amokachi ya bayyana hakan ne a hirarsa da kafar Telebijin ta Channels a ranar Lahadin da ta gabata, a sa’ilin da yake bayani biyo bayan cin Najeriya hudu ba ko daya da kasar Portugal ta yi, a wasan sada zumunta na kasa da kasa da aka yi a satin da ya gabata.

Saidai duk da wannan abu da ya faru da kungiyar kwallon Super Eagles din babu alamun hukumar NFF din za ta sallami Kocin Super Eagles din wato Peseiro.

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa na Paris Saint Germain dan kasar Kamaru, mai suna, Modeste M’Bami , ya mutu a ranar Lahadi sanadiyyar bugun zuciya. Ya rasu yana da shekaru 40 a duniya. A lokacin da yake raye, yayi wasannin kwallon kafa a kasashen Saudi Arabiya, Sin da kuma Sifaniya kafin ya yi ritaya a shekarar 2016.

Saurari cikakken rahoton Abdulwahab Muhammad: