Akalla kiristocin Najeriya 10,000 ne za su tafi ziyarar bauta kasashen Isra’ila da Jordan

Hukumar jin daɗin Kiristoci masu ziyarar bauta NCPC ta bayyana cewa akalla kiristoci 10,000 ne za su tafi ziyarar bauta kasashen Isra’ila da Jordan a 2022.
Hukumar ta Kuma ce za a fara jigilar matafiyan daga ranar 31 ga watan Mayu.
Shugaban hukumar Yakubu Pam ya fadi haka ranar Asabar a rangadin tashoshin jiragen sama da yake yi a Yola babban birnin jihar Adamawa inda daga nan ne za a fara jigilar matafiyan zuwa waɗannan ƙasashe.
Pam ya ce ya gamsu da shirin da hukumar tashar jirgin saman ta yi sannanya kara da cewa a bana mutum 400 daga jihohin Adamawa da Taraba ne za su tafi ziyarar bauta ɗin daga jihohin Adamawa da Taraba.
Pam ya ce bana an hada da Jordan a cikin wuraren da matafiya za su ziyarta saboda a wurin ne Yahaya mai baftisma ya yi wa Yesu Almasihu baftisma sannan a wannan wurin ne Annabi Musa ya yi wafati sannan kuma “Daga Jordan ne aka dauki Annabi Elijah zuwa sama.
Ya Kuma mika godiyarsa ga gwamnatin jihar Adamawa bisa goyan bayan da ta rika bai wa hukumar daga shekarun da suka gabata zuwa yanzu.