Akalla ƴan mata miliyan 10 basa makarantar boko a Najeriya – UNICEF

Shugaban sashen ayyuka na ofishin UNICEF dake jihar Kano Rahama Farah ya bayyana cewa akwai yara miliyan 18.5 dake gararamba a titunan kasar nan ba tare da suna makarantar boko ba inda aka tabbatar akwai yara mata miliyan 10 a Najeriya.

Farah ya fadi haka ranar Laraba a taron tattauna inganta ilimantar da yara mata da aka yi a jihar Kano.

Ya ce alkaluman adadin yawan yaran da basu makarantar boko da aka fitar abin tadhin hankali ne a kasar nan.

Taron inganta ilimin yara mata na daga cikin horon da aka yi wa ‘yan jarida daga jihohin Kano da Katsina.

” Zuwa yanzu akwai yara miliyan 18.5 din da basu makarantar boko inda kashi 60% ko kuma sama da miliyan 10 daga cikin su mata ne.

“Daga cikin mata miliyan 10 din da basu makaranta mafi yawan su daga yankin Arewacin kasar nan suke.

“Hakan ya kara fadada gibin dai-daita jinsin mata da maza inda mace daya daga cikin mata hudu ne ke iya kammala karatun JSS a makarantar sakandare.

Farah ya ce aiyukkan ‘yan bindiga na daga cikin matsalolin da ya kara hana yara mata zuwa makaranta inda iyaye da dama a Arewacin kasar nan na tsaron aikawa da ‘ya’yan su mata zuwa makaranta.

Ya yi kira ga ‘yan jarida da su taimaka wajen yin kira ga gwamnati domin ware kudaden da za a bukata wajen inganta ilimin boko a kasar nan.

Nasarorin da Shirin GEP3 ya samu a kasar nan.

Shirin ‘Girls Education Project 3 (GEP3)’ da kungiyoyin bada tallafi da kasar UK suka yi a kasar nan ya taimaka wajen samun karin miliyan 1.4 na mata dalibai a makaranta a Arewacin kasar nan.

Fara ya ce idan har aka ci gaba da Shirin sannan aka hada hannu da gwamnati, iyaye, malaman adini da sarakunan gargajiya za a cin ma burin ganin cewa Yara mata sun samu Kuma sun kammala karatun Boko.

Ya ce a dalilin Shirin kakanan hukumomin 34 a jihar Katsina sun tsaro matakai domin kare dalibai mata a makarantu a jihar.

“Akalla makarantun sakandare na JSS a jihar sun taro wadannan matakai sannan sun horar da ma’aikatan su a jihar.

A jihar Kano an horar da manbobin kwamitoci 300 sannan makarantun sun tsaro matakan samun kariya a jihar.