AI BARI BA SHEGIYA BA CE: Nnamdi Kanu ya roƙi magoya bayan sa kada su tada buyagi a kotu

Shugaban Kungiyar Rajin Neman Kafa Ƙasar Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, ya roƙi magoya bayan sa cewa su yi wa Allah kada su tada buyagi a harabar Babbar Kotun Tarayya, Abuja, idan an je shari’ar sa a mako mai zuwa.

A ranar 18 Ga Janairu ce Babbar Mai Shari’a Binta Nyako za ta yanke hukuncin ko Kanu na da gaskiya ko a ci gaba da shari’a.

Yayin da ake shirin zaman kotun, lauyan Kanu Ifeanyi Ejiofor ya same shi a Hedikwatar SSS inda ya ke tsare a Abuja, su ka tattauna yadda zaman kotun zai kasance.

Bayan dawowar sa daga wurin Kanu, lauya Ejiofor ya sanar cewa Kanu ya na gaishe da ɗimbin magoya bayan sa na cikin gida da na sauran ƙasashen duniya.

Sai dai kuma ya yi roƙon cewa kada su tada buyagi a harabar Babbar Kotun Tarayya a ranar zaman kotun.

“Kanu ya ce ya na roƙon magoya bayan sa su bi doka, su natsu, su nuna ɗa’a. Kuma kada su tada hankali ko tarzoma, hauragiya ko buyagi.”

Ejiofor dai ya ce ya na ji a jikin sa cewa Kanu, wanda ya riƙa kira da suna Onyendu, zai yi nasara a ranar.

PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa Nnamdi Kanu ya kai ƙarar Buhari ga jakadun Amurka da na Birtaniya.

Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Taratsin IPOB Nnamdi Kanu, ya rubuta wa Jakadar Amurka a Najeriya, Mary Beth Leonard wasiƙa, mai ɗauke da ƙorafin neman ta tura wakili domin ya zauna ya kalli zaman shari’ar sa da ake yi a Babbar Kotun Tarayya, Abuja.

Kanu na fuskantar tuhuma a gaban Mai Shari’a Binta Nyako ta Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.

Haka kuma ya rubuta ya rubuta irin wannan wasiƙa ga Jakadan Birtaniya a Najeriya, Catriona Laing, ita ma ya na roƙon ta aika wakilai domin su kalli shari’ar sa a mako mai zuwa.

Za a ci gaba da tuhumar cin amanar ƙasa da zargin ta’addancin da ake yi wa Kanu a ranar 18 Ga Janairu.

Har yanzu dai ya na tsare a Hedikwatar DSS tun cikin watan Yuni, 2021, bayan kamo shi da aka yi daga ƙasar Kenya. Wannan kamowa ce lauyoyin sa ke cewa “garkuwa” ce aka yi da shi.

Lauyan Kanu mai suna Ifeanyi Ejiofor ne ya rubuta wa Amurka da Birtaniya wasiƙar a ranar 11 Ga Janairu.

Takardar dai ta nemi a yi wa Kanu adalci a tuhuma da shari’ar da ke yi da shi.

Lauyan ya ce akwai siyasa a cikin shari’ar Kanu, shi ya sa su ke buƙatar Amurka da Birtaniya su sa-ido a shari’ar.

Cikin wasiƙar, lauyan ya nuna damuwa kan kalaman Shugaba Muhammadu Buhari kan Kanu, inda a hirar da NTA ta yi da shi ya bayyana dalilin da ya sa ba zai tsoma baki a saki Kanu ba.

A hirar dai Buhari ya ce an bai wa Kanu damar kare kan sa, maimakon ya riƙa surfa wa Najeriya zagi daga waje.

“Ba zai yiwu ya koma daga wata ƙasa ka na aikata ayyukan cin amanar ƙasa ba, sannan an kamo ka, ka ce ba za ka girbi abin da ka shuka ba.” Inji Buhari a cikin tattaunawar.

Dalilin Ba Ya Ba Ba Zan Tsoma Baki A Saki Nnamdi Kanu Ba -Buhari:

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ba zai tsoma baki ya ce a saki Nnamdi Kanu ba, saboda yin hakan katsalandan ne a cikin fannin shari’a.

Haka Buhari ya furta a wata tattaunawa da aka yi da shi a Gidan Talabijin na Channels, wadda aka nuna a ranar Laraba da dare.

“Akwai hukuma ɗaya wadda ba zan taɓa yi mata katsalandan ba. Ita ce ɓangaren shari’a.” Inji Buhari.

“Mun ba shi damar da zai kare kan sa a Najeriya, maimakon ya riƙa surfa mana zagi daga Turai.”

Da ya ke magana, Buhari ya ce ba za a saki Nnamdi Kanu ba, sai dai ya kare kan sa a kotu kawai.

“Masu cewa a saki Nnamdi Kanu, to ba za a sake shi ba, saboda ba zai yiwu ka riƙa aika saƙonnin da ba gaskiya ba ne a kan tattalin arzikin ƙasa da tsaron ƙasa, sannan kuma ka ce wai ba za ka girbi abin da ka shuka ba.”

Shari’ar Kanu Da Ziyarar Dattawan Igbo Fadar Shugaban Ƙasa:

Watanni biyu da suka gabata ne wannan jarida ta buga labarin yadda dattawan ƙabilar Igbo su ka faɗi ba nauyi, su ka tashi ba nauyi a gaban Buhari, yayin ziyarar neman a saki Kanu da suka kai Fadar Shugaban Ƙasa.

Shugaba Muhammadu Buhari ya shaida wa wasu dattawan ƙabilar Igbo cewa ba zai shiga hurumin ɓangaren shari’a ba, domin ya saki Nnamdi Kanu, wanda a yanzu batun tuhumar da ake masa na kotu.

Buhari ya yi wannan furucin ne yayin wa wasu gungun manyan dattawan ƙabilar Igbo su ka kai masa ziyarar roƙon ya saki Nnamdi Kanu da ke tsare.

Nnamdi Kanu, wanda shi ne Shugaban Ƙungiyar IPOB masu rajin ɓallewa daga Najeriya ko da tsiya, ya shiga hannun hukuma ne yayin da aka kamo shi daga waje, bayan ya tsallake ƙasar nan daga belin sa da aka bayar.

Shugaban tawagar mai suna Mbazulike Amaechi, ya shaida wa Buhari cewa sun zo ne domin su roƙe shi alfarmar ya saki Nnamdi Kanu domin a samu zaman lafiya a yankin Kudu maso Gabas.

Mbazulike, wanda dattijo ne mai shekaru 93 a duniya, ya shaida wa Buhari cewa a cikin ministocin da aka yi a Jamhuriya ta ɗaya, shi kaɗai ne ya rage a duniya.

“Ina roƙon Shugaban Ƙasa ya yi alfarmar cewa idan ya saki Kanu, ni da kai na zan sa masa takunkumin hana shi yin irin kalaman ɓatuncin da ya ke yi.

“Na kasance dattijon da ake girmamawa a Yankin Kudu maso Gabas sosai. Ina roƙon a ba ni shi domin dama ce ta samar da zaman lafiya a yankin mu.

“Ya mai girma Shugaban Ƙasa, yankin mu ya shiga cikin gagarimar matsala saboda tashe-tashen hankulan da ake yi dalilin IPOB.

“Harkokin tattalin arziki sai ja baya su ke yi. Ga kuma harkar ilmi ta shiga garari. Matsalar tsaro kuma sai ƙara ƙamari ta ke yi.

“Na yi amanna da cewa a bi matakin diflomasiyyar siyasar cikin gida a wanzar da zaman lafiya a yankin shi ne mafi alheri, ba amfani da ƙarfin soja ba.

“Ba zan yi fatan na mutu na bar yankin mu cikin tashin hankalin da ya ke ciki ba a yanzu.

“Shugaban Ƙasa wannan dama ce gare ka cewa idan ka saki Kanu, ka zama shugaban da ya samu yankin mu ciki rikici, amma ya wanzar da zaman lafiya a yankin.”

Jawabin Buhari Ga Dattawan Ƙabilar Igbo Masu Roƙon Ya Saki Nnamdi Kanu:

Buhari ya shaida wa Mbazulike cewa ba zai so ya shiga hurumin ɓangarorin gwamnati ba, domin fannin Shari’a ba ɓangaren sa ba ne.

“Na tabbata babu wanda zai iya fitowa ya ce a tsawon shekaru shida da na yi a kan mulki, na yi wa ɓangaren Shari’a katsalandan ko sau ɗaya.

“Da farko dai ina jinjina maka a matsayin ka na dattijo wanda ya haura shekaru 90, amma kaifin tunanin ka garau ya ke. A yanzu haka akwai masu rabin shekarun ka a duniya, amma idan su na magana, ba su iya kama-tasha.

“Kuma ina yi maka ta’aziyyar mutuwar matar ka, wadda ta bar duniya kwanan nan.

Batun Kanu kuwa abu ne mai matuƙar wahalar da zan sa baki a kai. Amma zan duba na ga mai iya yiwuwa.

“Lokacin da ya tsare daga belin da aka bayar na shi, da aka kamo shi aka dawo da shi. Ai gata mu ka yi masa da muka ce idan
ya na da wata jayayya, ya tafi kotu.”

Mbazulike ya sha wa Buhari alwashin cewa sakin Nnamdi zai samar da zaman lafiya a yankin Kudu maso Gabas.

“Ni ba ni goyon bayan IPOB, ina ƙaunar kasancewar Najeriya dunƙulalliyar ƙasa ɗaya.”

Tawagar dai ta mutum shida ce, ciki kuwa har da Chukwumeka Ezeife.