Adana abinci a robobin magani da suka kare na da matukar hadari ga lafiyar mutum – Gargadin NAFDAC

Hukumar kula da ingancin magunguna da abinci ta ƙasa NAFDAC ta gargadi mutane da su daina adana danyen abinci a roban maganin da ya kare, cewa yin haka na cutar da lafiyar mutum.

Shugaban hukumar Christianah Adeyeye ta yi wannan gargadi a taron wayar da kan mutane sanin illar dake tattare da yin haka da aka yi a fadar sarkin Onitsha Alfred Achebe dake jihar Anambra.

Adeyeye wacce shugaban sashen gudanar da bincike kan magungunan a hukumar Ngozi Onuora ta wakilta a taron ta ce akwai guba a cikin robar magani da ko an wanke cu gubar shi fita kwata-kwata.

Ngozi ta ce a dalilin haka ajiye abinci a cikin robobi irin haka na cutar da lafiyar mutum.

“Muna kira ga mutane da su daina zuba man gyada a cikin galan din da ake zuba kananzir a ciki, a daina amfani da sinadarin bromate wajen yin buredi, a daina amfani da sinadarin wajen nika ayaba, mangwaro da sauran su.

Ta kuma kara yin kira ga mutane da su rika siyan magani a ingantattun shagunan siyar da magani ba a wurin masu talla a kasuwa ba.

Da yake tofa albarkacin bakinsa sarkin Onitsha Achebe ya yi kira ga jami’an tsaro da su mara wa sarakunan gargajiya baya wajen yaki da ta’ammali da muggan kwayoyi a garin Onitsha.

Ya ce sarakunan gargajiya sun taka muhimmiyar rawa wajen yaki da sha da safarar muggan kwayoyi amma nasarorin da aka samu za su daure idan jami’an tsaro suna yin tafiyar tare da su.