ADAMAWA TA KWASHI ‘YAN KALLO: Binani ta kamo hanyar tururmusa ƙarti 14 a kokawar ƙwace kujerar gwamna

Alamomi daga sakamakon zaɓen Jihar Adamawa na gwamna sun nuna Aishatu Ɗahiru, wadda aka fi sani da Binani ce kan gaba wajen yawan ƙuri’u da rata mai yawa.
Binani wadda ke takara a APC, ta na ci gaba da gaggabzar mazaje 14 masu takara da ita.
Sai dai rahotanni sun nuna cewa Gwamna Pintiri na PDP ke biye da ita, amma shi ma tuni ta yi masa jina-jina, kuma ta gurgunta shi.
Ana ganin babu wani tsimi ko wata dabara, sai Binani ta yi nasara a zaɓen, wanda a yanzu haka ana tattara sakamakon zaɓe daga cibiyar tattara sakamako ta ƙananan hukumomi zuwa Cibiyar Tattara Sakamakon Zaɓe ta Yola, babban birnin jihar.
Tuni dai aka fitar da ƙananan hukimomi 10, daga nan kuma aka dakata. Akwai ƙananan hukumomi 21 a Adamawa.