Abubuwan da ya kamata ku sani game da e-Naira wanda Babban Bankin Najeriya CBN ya kirkiro – Binciken DUBAWA

Ba za’a iya kuzantawa ko kuma aki jinjinawa mahimmancin cigaba na fasaha da aka samu a fannonin rayuwa ba. A fanin tattalin arziki da hadahadar cinikayya da kudi, sauyawar da aka yi zuwa amfani da sabbin fasahohi ya taimaka wajen ajiya da adana kudi da kasuwanci. dalilin haka ya sa ake samun cigaba ta hanyar kirkiro wasu sabbin hanyoyin gudanar da hadahadar cinikayya da kudi.

Sakamkon wadannan manyan sauye-sauyen da aka samu mutane na iya amfani da kati su cire ko su tura kudi ta yin amfani da POS a daidai wurin da suke cinikayya ba tare da sun yi amfani da ATM a bankuna ba ko kuma wasu wuraren.

Bugu da kari, bunkasar da ake samu a wannan fannin na kara ingantuwa domin CBN a shirye ta ke ta kadamar da kudaden da za’a iya amfani da su a yanar gizo, wanda ake kira eNaira. Dan haka mun yi binciken tambayoyi masu mahimmanci ga jama’a wadanda kuma za’a so jin amsoshinsu alal misali, wace rawa eNaira za ta taka a al’umma? Wani alfanun ‘yan kasa za su samu daga amfani da shi?

Mene ne eNaira?

eNaira kudi ne da babban bankin Najeriya ta samar wanda zai kasance kudin da za’a iya amfani da shi a duniyar yanar gizo ta yadda ba sai an yi amfani da takardar naira ba. A Najeriya, darajar eNaira za ta kasance daidai da ta naira da ake hada-hada da shi. Daya daga cikin abubuwa masu ban sha’awa kan wannan kudin dai shi b ne abu kudin ruwa, sa’annan wurin kera shi an yi amfani da fasahar da ke nadar duk wata hada-hadar kudin da ake yi. Wannan na nufin cewa baza’a iya kwafan eNaira ko kuma yin na bogin shi ba saboda kowace takardar na da alama ta musamman da ta banbanta ta da sauran.

Yaya amincin eNaira?

Duk wata harka ta kudi, aminci na da mahimmancin gaske. Hakan ne ya sa wajen kirkiro eNairar aka kera shi yadda zai iya kaucewa duk wani hadarin da ya danganci tantance sahihancin shi ta baiwa kowanne ingantacciyar alama. An yi nasarar cimma wannan buri ne ta yin amfani da fasahar da ake kira blockchain wadda ke hana sata da zamba. Dan haka babu shakka yawancin ‘yan kasuwa za su karbi eNaira domin ba wanda zai iya kwafa ko yin na bogi.

Yaya za’a iya samun eNaira?

Babban bankin Najeriya (CBN) za ta fitar da shi daki-daki ne. Na farko za ta baiwa cibiyoyin kudi irin su banki. Daga nan sai bankin ta sayarwa kwastamominta. Misali idan mutun ya yi cinikin kasa da 50,000 a rana, ba ya bukatar asusun banki, iyaka ya yi amfani da lambar wayar da aka yi amfani da ita wajen samun lambobin NIN dan sayen eNairar. Idan kuma kana so a cire kudin da ya wuce 50,000 wanda kuma ya wuce milliyan dayan da aka kayyade a matsayin iyakar kudin da mutun zai iya cirewa kowace rana, ana bukatar BVN tare da lambar wayar.

Babban bankin na da matakai tsaurara na gane kwastamomi ko kuma masu amfani da wadannan sabbin fasahohin, dan tabbatar wa jama’a cewa eNairar na da aminci da saukin sha’ani.

Me ya sa zan yi amfani da eNaira?

Amfani da eNaira na da arha. Aika kudi tsakanin bankuna kyauta ne ga duk mai asusun, kuma wannan rangwame babban alfanu ne domin ‘yan kasuwa ba za su biya ko sisi ba wajen shigar da kudi ko fitar da shi. Ke nan babu kudaden ma’amala sai dai ingancin matakan kare ajiyar kudi.

Yaya za’a tafiyar da batun aiken dala zuwa eNaira?

Za’a sanya eNaira cikin hada-hadar kasuwannin CBN kuma wannan zai saukake karbar dalolin da ake turowa Najeriya. Wannan kudin zai iya zuwa daga CBN kanta wadda za ta tura eNairar zuwa Kungiyar Musayar Kudi ta Duniya (IMTO). Misal,i mai zama a kasar waje, zai iya tura dalan Amirka 100 zuwa IMTO, su kuma sais u sayi eNaira daga bankin da suke hulda da shi. Nan take dala 100 zai koma eNaira kuma a farashi mai rangwamen gaske. Wannan babban alfanu ne wanda eNaira zai bai wa kwastamomi.

Abubuwan da za’a iya yi da eNaira

Duk bangarori biyun da za su sa ko za su karbi kudi a bankunan Najeriya za su iya amfani da eNaira. Wannan na nufin dan kasuwan da ke amfani da bankin UBA a Burkina Faso za su iya biyan kudaden shigar da kaya a Gambia da eNaira. Wannan ne matakin da zai biyo bayan kaddamar da eNairar a cibiyoyin kudi, dan ta yin haka za a gina yanayin da zai mayar da eNaira ginshikin cinikayya.

Bugu da kari CBN ta bayyana cewa eNaira zai kawo galibin ‘yan Najeriya cikin yanayin tattalin arziki a hukumance musamman irin wadanda ke da wayar hannu amma ba su da asusun banki. Ana kuma iya amfani da eNaira wajen biyan albashi, da saye da sayarwa. Misali, mai gyaran wutar lantarki zai iya karbar kudin shi a waya ya kuma yi amfani da shi ya duk harkokin da yak e so.

Mene ne hadarin shi?

eNaira na kan yanar gizo-gizo, bayanan BVN da NIN duk su ma suna kan yanar gizon dan haka hadarin samun masu zamba bas hi da yawa. Haka nan kuma CBN ta tabbatar da amincin shi ta yin amfani da ingantattatun akamu. Baki daya cigaba ce mai amfani musamman wajen komawa al’ummar da ba ta hada-hada da takardun kudi kuma za ta rage farashi ta kuma inganta karfin aiki.

A karshe

Duk da cewa shugaban babban bankin Najeriya Godwin Emefiele ya tabbatar da cewa za’a kaddamar da eNaira nan ba da dadewa ba, bankin ya dage matakin kuma bai riga ya sanar da ranar da za’a yi ba. A cewar gwamnan bankin eNaira zai kasance na farko irin shi a nahiyar Afirka.