Abubuwan da ya kamata Dauda Kahutu Rarara ya koya daga rayuwar Davido, Daga Buhari Abba

A cikin watan Satumbar shekarar 2020 ne fitaccen mawakin siyasar nan na Hausa ɗan asalin jihar Katsina, Dauda Kahutu Rarara, wanda ya yi fice wajen yi wa Shugaba Muhammadu Buhari waka, ya ce ba zai sake yi masa waka ba sai an biya shi.

Rarara ya bayyana cewa zai sake yi wa Shugaba Buhari waka ne kawai idan talakawan da suka zaɓe shi kowannensu ya mika masa ₦1000.

Ya ce ya yanke shawarar hakan ne sakamakon yadda ake yada jita-jita a shafukan sada zumunta cewa Shugaba Buhari ya gaza a mulkinsa shi ya sa ya ce ba zai sake yin waka don talakawa su ji dadi ba sai sun biya kudi.

Wannan roko na Dauda Kahutu Rarara ya yi ga waɗanda su ke da ra’ayinsa ya sanya ya samu Naira Miliyan 57 a cikin ƙasa da awanni 24 kamar wata majiya ta kusa da shi ta tabbatar mana.

Haka kuma Allah ne ya san yawan adadin miliyoyin kuɗin da ƴan Najeriya su ka turawa Dauda Kahutu Rarara kawo wannan lokaci. Amma wani abin mamaki da ban al’ajabi ga mawakin shi ne hanyar da ya bi ya yi tasarrufi da wadannan miliyoyin kuɗin.

A bayyane ta ke kowanne ɗan adam yana da ƴancin yin amfani da dukiyarsa yadda ya ga dama domin mallakinsa ce, amma akwai bukatar aiki lura tare da kuma da yin abin da ya dace da dukiya ga mai ita.

Al’ummar Najeriya da ma duniya sun san halin da jihar Katsina ke ciki wacce ita ce jihar Dauda Kahutu Rarara ta haihuwa, domin jihar na daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da suka fi fama da matsalolin tsaro da ake alakantawa da yan fashin daji a wannan lokaci.

Hakazalika jihar ta Katsina na da ɗimbin matsaloli da su ke kokarin kai ta ƙasa a ɓangaren tattalin arziki da cigaba. Domin akwai dubban ƴan gudun hijira da yan fashin daji su ka tarwatsa da matsalar ingantaccen ilimi a yankunan karkara da matsalar rashin ɓangaren kiwon lafiya ga al’ummar da su ke zaune a yankuna irin wanda Rarara ya fito.

A ɗaya ɓangaren kuma yankunan karkara musamman yankin Karaɗuwa (Kudancin Katsina), na fama da matsalar kashe-kashen mutane da ƴan bindiga ke yi tare da sace mutane don karbar kudin fansa .
Amma a maimakon Dauda Kahutu Rarara ya yi amfani da waccan da dukiya da ya samu daga masoyansa wajen taimakon dubban jama’ar Katsina da masifar rashin tsaro ta tagayyara tare da mayar da ƴaƴa marayu, mata su ka zama zawarawa, manoma su ka rasa gonakinsu, fatauci ya gagara a tsakankanin ƴan kasuwa, iyaye su ka daina tura ƴaƴansu makaranta saboda fargabar sace su, sai aka ga mawaƙin ya ɓige da rabawa jaruman Kanywood motoci a birnin Kano.

Ba a ce kar ya rabawa ƴan Kanywood motoci ba domin haka ya ga fi dacewa a nazari da hange irin na sa, amma ya fi dace a ce ya ɓullo da wata gidauniya ta musamman da za taimakawa talakwa da marasa ƙarfi ko da masifar rashin tsaro ta jefa cikin halin wayyo ni Allah ko da a iya ƙananan hukumomin Bakori da Danja ne. Domin babu ko shakka hakan zai sanya al’umma su yi wa Rarara kallon wayayyen mutum wanda ya damu da halin da al’ummar sa ta ke ciki. Amma kash sai mawaƙin ya ɓige da son ya birge duniya ta hanyar yin bajintar rabon motoci.

Shekara guda watanni biyu da wannan batun tara kudade da aka yiwa Dauda Kahutu sai ga shi katsama shahararren mawakin nan, David Adeleke Adedeji wanda ake kira da Davido ya ce zai ba gidajen marayu da ke faɗin Najeriya zunzurutun kudi har naira miliyan 250, kwatankwacin dalar Amurka dubu dari 608, bayan da magoya bayansa suka aika masa da kudi.

Tun da farko wannan mawaki ya nemi magoya bayansa da suka yi intifakin cewa ya yi mu su wakar da ta kasance bakandamiyya da su tura masa da kudi zuwa wani asusun ajiyar kudi da ke dauke da sunansa.

Davido wanda ake yi wa kallon daya daga cikin manyan shahararun mawakan Afrika, ya ce ya gabatar da kokon barar ne cikin raha da nishaɗi amma yawan wadanda suka amsa kiran nasa ya zarce yadda ya rika tsammani.

Mai karatu ka sani shi Davido ya fito daga yankin da ya ke yanki ne mafi karfin tattalin arziki a Najeriya, haka kuma jihar da ta ke asalinsa wato jihar Osun ba ta fama da irin matsalolin da jihar Katsina ke fama da su. Amma ya yi wannan kyakkyawan tunanin wanda ya ɗauki hankalin duniya tare da samun yabo da jinjina. Wanda na imanin da a ce haka Rarara ya yi babu shakka zai ƙara tasiri ga miliyoyin al’ummar da ke amfani da harshen Hausa a faɗin duniya. Haka kuma zai ƙarawa dukkanin wata jam’iyyar siyasa da ya ke cikinta farin jini a tsakanin al’umma.

Haƙiƙa Dauda Kahutu Rarara ya kamata ya fahimci cewa ba wai ana samun yabo da jinjina ne ta hanyar yin burga ba. Ya kamata ya sani cewa ajiye ƙwarya a gurbinta shi ya fi komai fa’ida.

Buhari Abba – [email protected]