Abubuwan al’ajabi dangane da fatattakar da Morocco ta yi wa Spain daga Qatar 2022

Maganar irin ƙoƙarin da ƙasar Morocco ta yi kafin fitowar ta zuwa gasar Kofin Duniya na Qatar 2022, ya zama tarihi. Yanzu maganar da ake yi shi ne irin bajintar da ‘yan wasan ƙasar su ka yi har su ka kori Spain, wadda ake ganin ta na ɗaya daga cikin ƙasashen da ake wa kallon za ta iya cin kofin.

Morocco ta kafa tarihin zama ta ɗaya a rukunin su da maki 7, abin da wata ƙasar Afrika ba ta sake yi ba tun da Najeriya ta yi irin haka a 1998, a Faransa.

Bayan tashi wasan a kunnen-doki, an ƙara mintina 30, daga nan kuma aka bada ƙofar bugun daga kai sai mai tsaron gida.

‘Yan wasan Spain uku sun buga ba su ci ba. Na farko ta bugi ƙarfe, na biyu da na uku kuma duk mai tsaron gidan Morocco ya ture su.

Ashraf Hakimi, mai tsaron bayan PSG wanda ya jefa ƙwallon ƙarshe da ta bai wa Morocco nasara, tashin ƙasar Spain ne, tun ya na ƙaramin yaro. A birnin Madrid ya taro ya na yaro a cikin talauci. Iyayen sa baƙin hijira ne daga Morocco, yayin da mahaifiyar sa ta riƙa yin sharar titi, shi kuma mahaifin sa tallar kaya kan titi ya riƙa yi.

A cikin irin wannan rayuwar talauci Ashraf Hakimi ya taso, kuma a haka iyayen sa su ka riƙa kula da shi, har ya fara wasan ƙwallon da ya samu ɗaukaka, har ya buga wasa a Real Madrid.

Ashraf ya samu arzikin da a yanzu abin da ya fi maida hankali shi ne kyautata wa iyayen sa. Domin ko a wasan su kafin doke Spain, an nuno Hakimi ya rungume mahaifiyar sa bayan tashi daga wasa a cikin sitadiyan.

Kafin a fara bugun daga kai sai mai tsaron gida, an nuno ‘yan wasan Morocco sun yi da’ira su na karanta Suratul Fatiha.

Ganin cewa ita kaɗai ce ƙasar Larabawa da ta rage a gasar, bayan fitar da irin su Qatar da Saudiyya da sauran, kusan Larabawa kakaf sun koma goyon bayan Morocco. Hatta Sarakunan da ke mulkin Qatar da iyalan su, duk an nuno su na goyon bayan Morocco.

Haka nan Afirka yanzu kowa Morocco ya ke so, saboda ita kaɗai ce ta rage daga cikin ƙasashen Afrika da su ka je gasar Qatar 2022.

Wannan nasara da Morocco ta yi kan Spain ya ƙara janyo wa ƙasar martaba, Larabawa na ta sayen rigar ‘yan wasan ƙasar su na yin ado da ita.