A saka dokar ta baci a fannin kiwon lafiya a kasar nan – Likita

Shugaban kungiyar likitocin hakora MDCAN Victor Makanjuola ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta saka dokar ta baci a fannin kiwon lafiyar kasar nan saboda matsalolin da fannin ke fama da su.

Makanjuola ya ce daya daga cikin matsalolin da fannin ke fama da su shine ficewar likitoci daga kasar nan zuwa kasashen waje.

Ya ce hakan na da alaka ne da matsalar rashin tsaro, rashin biyan likitoci albashi mai tsoka sannan da rashin zuba ingantattun kayan aiki a asibitocin kasar nan.

“A dalilin haka na yi kira ga gwamnati da ta saka dokar ta baci domin kawo karshen matsalolin dake gurguntar da fannin.

“Fannin kiwon lafiyar kasar nan na fama da likitocin da suka hada da yajin aikin likitocin da ya kai sama da wata daya yanzu, wasu kungiyoyin ma’aikatan lafiya na barazanar fara yajin aikin.

‘Yan siyasa da shugabanin kasar nan basa zuwa asibitocin kasar nan a duk lokacin da basu da lafiya saboda sun San cewa ba za su samu ingantacen kula ba.

“Kuma har yanzu kasan na cikin kasashen dake fama da yawan mace-macen jarirai da mata wajen haihuwa.

“Idan fannin lafiya na fama da irin wadannan matsaloli kamata ya yi gwamnati ta mike tsaye wajen ganin ta kawo karshen matsalolin dake gurguntar da fannin.

Makanjuola ya koka da yadda ake daukan likitocin da suke da digirin PHD fiye da likitocin da suma suka kware a dalilin shekarun da suka yi suna aiki.

Ya ce yin hakan bai kamata ba domin ana rasa kwararrun ma’aikata a fannin.

Daga karshe Makanjuola ya yi kira ga gwamnati da ta kawo karshen rikici, garkuwa da mutane domin zamar da zaman lafiya a kasar nan.

Ya ce yin haka zai taimaka wajen hana yawan ficewar likitoci daga kasar nan zuwa kasashen waje.

Biyan likitoci albashi mai tsoka, zuba ingantattun kayan aiki, inganta tattalin arziki na cikin hanyoyin da zai taimaka wajen inganta fannin kiwon lafiyar kasar nan.