A KIMTSA A SHIRYA: Matafiya biyu sun shigo da mummunar korona samfurin ‘Omicron’ cikin Najeriya -NCDC

Hukumar Daƙile Cututtuka Masu Yaɗuwa (NCDC) ta bayyana cewa cutar korona samfurin Omicron mai saurin maƙure mutum ta kashe, ta shigo Najeriya.

Cikin jawabin da Babban Daraktan NCDC, Ifedayo Adetifa ya fitar a ranar Talata da dare, ya ce an samu wasu matafiya mutum biyu da su ka shigo da cutar daga Afrika ta Kudu.

Ya ce an tabbatar da haka ɗin bayan wani gwaji da aka yi a Babban Ɗakin Gwajin Abuja.

Wannan sanarwa ta zo ne kwanaki biyu bayan ƙasar Kanada ta bayyana cewa an matafiya biyu daga Najeriya ɗauke da cutar korona samfurin Omicron a Kanada.

A kan haka, NCDC ta ce ta ƙara miƙewa tsaye wajen tsaurara matakai.

Sannan kuma ta na ƙara kira da a gaggauta zuwa ana yin rigakafin korona.

Wannan jarida a ranar Talata ta buga labarin cewa Samfurin ‘Omicron’ mai saurin maƙure mutum ta kashe ba ta iso Najeriya ba.

Hukumar Daƙile Cututtuka Masu Yaɗuwa (NCDC) ta bayyana cewa sabuwar korona mai saurin maƙure mutum ta kashe farat ɗaya ba ta shigo Najeriya ba.

Sabuwar cutar ta korona samfurin Omicron (SARS-Cov-2) dai a yanzu ta tashi hankulan duniya, inda a na ta ɓangaren Najeriya ta haramta wa ‘yan ƙasar nan shiga ƙasahe irin su Afrika ta Kudu, Botswana, Italy, Jamus, Belgium da Birtaniya, inda cutar ta ɓulla.

Cikin wata sanarwa da NCDC ta fitar raanr Asabar da dare, Darakta Janar na hukumar, Ifedayo Aderifa ya ce cibiyar NCDC na sa-ido tare da lura da halin sa ake ciki kada cutar ta shammaci ƙasar nan.

Ya ce kuma duk halin da NCDC ke ciki, za ta riƙa sanar da jama’a

Omicron: Korona Mai Saurin Kisa: NCDC ta ce har yanzu dai babu wani rahoton wannan sabuwar cuta ta yi kisa a Najeriya, amma fa an gano sagwangwaman ta har guda 126.

“Gano sagwangwaman wannan sabuwar cuta tare da gami da fantsamar cutar a Afrika ta Kudu, hakan ya tabbatar da cewa wannan cutar ta na saurin yaɗuwa a cikin mutane.

Amurka Da Turai Sun Ƙaƙaba Wa Ƙasashen Afrika Takunkumin Hana Zirga-zirga Cikin Su:

Wasu fitattun ‘yan Najeriya ciki har da Shugaban Bankin Bunƙasa Afrika (AIB), Akinwumi Adesina, sun yi tir da yadda Turai da Amurka su ka ƙaƙaba wa Afrika dokar shiga ƙasashen su, saboda an samu bayyanar cutar korona samfurin Omicron ta ɓulla a Afrika ta Kudu.

Alakija wadda ita ma ta yi wannan tir ɗin a hirar ta da BBC, ta ragargaji ƙasar Amurika da Turai bisa yi wa sauran ƙasashen Afrika kudin-goro, ake gallaza masu a kan laifin da ba kowace daga cikin su ta aikatawa ba.

“Alƙaluman masu bincike ya nuna cewa korona samfurin Omicron da ta ɓulla a Afrika ta Kudu, ta na saurin kama jikin mutum, kuma ta kan yi kisan farat-faɗa.” Inji Hukumar Kula da Lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya (WHO).

Baya ga Afrika ta Kudu, korona samfurin Omicron, ta bayyana a ƙasashen Isra’ila, Malawi, Botswana, Birtaniya, Jamus, Italy, Belgium, Hong Kong da wasu ƙasashe da dama.