“A gaban ido na ƙanina Sani ya rasu babu abin na iya yi”- Ɗangote

Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya baiyana yadda ƙaninsa, Sani Dangote ya rasu a gaban idanun sa.

A ranar Lahadin da ta gabata ne dai Sani Ɗangote, wanda shine Mataimakin Shugaban Rukunin Kamfanoni Ɗangote, ya rasu a wani asibiti da ke birnin Miami a ƙasar Amurka.

“A gaban ido na ƙanina Sani ya rasu babu abin na iya yi”- Ɗangote
Minista da Babban Sufeton Ƴan Sanda sun yaba da ingancin kayakin aikin da hukumar NPTF ta sayo

Yayin da ya tarbi Jagoran Jam’iya APC mai mulki, Bola Tinubu a gidansa da ke Kano a ranar juma’a, Ɗangote ya baiyana cewa a gabansa da maihaifiyarsu, da ƴaƴan Sani Allah ya karbi ransa.
Dangote ya ƙara da cewa, da su ka je asibitin, a lokacin da a ke duba marigayin, likitocin sun faɗa musu cewa nan da awa ɗaya zai rasu.
Ya ƙara da cewa lokacin da marigayin ya ke kwance an jona masa na’ura, “abin baƙin ciki da ciwo shine cewa mu na kallo ta na’ura har ya rasu. Wannan abu da tashin hankali ya ke. Daily Nigerian ta ruwaito.
“Amma haka Allah Ya tsara. Kuma kowa zai rasu. Ba wanda ya san wanene gawar fari. Ko mai kuɗi ko talaka. A matsayin mu na musulmai, mun yi imani da mutuwa.
“Mu na riƙon Allah da Ya jiƙansa da gafara.
“Mai girma Gwamna, mu na godiya da wannan karamci da ka ke mana. Mun gode sosai, Allah Ya saka da alheri”. A cewar Dangote.
A nashi jawabin, Bola Tinubu ya baiyyana cewa kuɗi ba zai iya siyan rayuwa ba, inda ya ce idan mutuwa ta zo ba abinda aka isa a yi.
Ya yi ƙira ga Dangote da sauran dangin marigayin da su dage da yi masa addu’a, in da ya ce ya zo Kano me domin yin ta’aziyar mamacin.

Tura Wa Abokai